Kiran tsagaita wuta a Gaza ya janyo rabuwar kai a tsakanin mambobin EU
Dole duniya ta nuna kyama kan abin da ke faruwa a Gaza — Red Cross
Babban jami’in harkokin kasashen ketare na Kungiyar Tarayyar Turai EU Josep Borrel ya bukaci tsagaita wuta a Zirin Gaza cikin hanzari, domin bayar da damar kai agajin gaggawa ga al’ummar Falasdinawa da rikicin ya rutsa da su.
Kiran na Josep Borrel ya gamu da shan suka daga bangaren wasu shugabannin kungiyar, inda Firaministan kasar Austria ya ce matakin neman a tsagaita wuta ya saba wa matsayar da EU ta cimma a ranar Asabar.
- Atiku zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Litinin — PDP
- Jirgin ruwa dauke da mutum 100 ya nutse a Kogin Binuwai
A nata bangaren kungiyar Red Cross da ke bayar da agajin gagawa ita ma ta yi kira da a gagauta kawo karshen wannan yakin a wani mataki na kauce wa mumunan bala’i da ka iya biyo baya, a daidai lokacin da Isra’ila ta kara tsananta kai hare-harenta.
Dole duniya ta nuna kyama kan abin da ke faruwa a Gaza — Red Cross
Red Cross ta bakin shugabanta ta ce dole duniya ta nuna kyama a kan abin da ke faruwa, ta kara da cewa yanzu haka a Zirin Gaza akwai mutane sama da miliyan biyu da ba su da wurin tserewa, kuma ana ci gaba da yi musu luguden wuta.
Red Cross da takwararta Red Crescent sun ce sun kaɗu game da umarnin da ojojin Isra’ila suka bai wa ma’aikata a asibitn Al-Quds da ke Gaza da su bar wajen.
Asibitin yana bai wa aƙalla mutum 14,000 mafaka da kuma ɗaruruwan marasa lafiya da ke samun kulawa.
Sanarwar da Red Cross ta fitar ta ce: “Asibitoci wuri ne na taimako da kuma neman mafaka, dole ne a kare su. Asibitin Al-Quds da ke Birnin Gaza na kula da ɗaruruwan masu rauni da kuma marasa lafiyar da ke jinya.
“Kwashe marasa lafiya, ciki har da waɗanda suke sashen kulawa akai-akai da kuma jariran da ke cikin kwalaba, ba zai yiwu ba a irin yanayin da ake ciki.
“Haka nan ma’aikatanmu sun bayar da rahoton wani hari kusa da asibitin da ke ƙara jefa rayuwar mutane cikin haɗari. Al-Quds na ƙarƙashin kulawar PRCS, gamayyar ƙungiyar Red Cross da Red Crescent da sauran cibiyoyin lafiya kuma dokar ƙasashen duniya ta ba shi kariya.”
Ta ƙara da cewa bai kamata a dinga “jefa ma’aikatan lafiya cikin halin tsaka mai wuya ba ta yadda za su bar marasa lafiya a kwance.”
Ita ma hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijira a yankin Zirin Gaza UNRWA ta bayyan halin ha’ula’in da al’ummar Gaza ke ciki na rashin wutar lantarki da abinci da ruwan sha, ta ce wannan matakin ya saba wa dokokin agaji na kasa da kasa.
Ya kamata a kai zuciya nesa — Paparoma
Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya yi kira ga bangarorin da ke fada da juna a yankin Gabas ta Tsakiya wato Isra’ila da Hamas da su kai zuciya nesa don kauce wa ci gaba da zubar da jinin fararen hula.
A jawabinsa yayin addua a majami’ar St. Peters da ke Vatican, Paparoma Francis ya kuma bukaci kungiyar Hamas da ta saki mutanen da take ci gaba da garkuwa da su.
Wannan bukata na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ta bukaci mazauna yankunan Zirin Gaza da su koma kudanci domin samun kayayakin agaji.
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar dubban Falasdinawa ne suka fasa dakunan ajiyar kayayyakin agaji da ke Gaza, inda suka kwashi fulawa da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.
Makonni 3 ke nan aka kwashe ana dauki ba dadi tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da luguden wuta kan Falasdinawa a Gaza.