Kiraye-kiraye goma masu girma daga Allah (2)

Masallacin Salihiyya, Wadi Addawasir, Saudiyya Fassarar Salihu Makera Huduba ta Biyu: Godiya ta tabbata ga Allah godiya mai yawa mai dadi mai albarka a cikinta. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa […]

Kiraye-kiraye goma masu girma daga Allah (2)

Masallacin Salihiyya, Wadi Addawasir, Saudiyya

Fassarar Salihu Makera

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Allah godiya mai yawa mai dadi mai albarka a cikinta. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne Tsira da Amincin Allah su kara tabbata  a gare shi da alayensa da sahabbansa da aminci da taslimi mai yawa.

Bayan haka, ku ji tsoron Allah kuma ku sani lallai kira na tara mai girma daga Ubangiji Wadatacce Abin godiya shi ne fadinSa Mai tsarki a Hadisin kudusi mai tsarki: “Ya ku bayiNa! Da dai na farkonku da na karshenku da mutanenku da aljanunku za su taru a fili guda su roke ni kuma in bai wa kowa abin ya roka, hakan ba zai rage koma daga cikin abin da ke wuriNa ba, face kamar yadda allura za ta rage idan aka tsoma ta a teku.”

Allahu Akbar! Me ya kai girman Allah! Kuma me ya kai tsananin wadatarSa? Duk yadda Allah Ya bayar, hakan ba zai rage komai daga abin da Ya mallaka ba. An karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Lallai damar Allah a cike take, ciyarwa ba ta rage ta da komai. Mai yawaita kyauta ne a dare da rana. Shin ba ku gani abin da Yake ciyarwa (bayarwa) tun daga lokacin da Ya halicci sammai da kasa, kuma lallai shi abin da yake damarSa bai ragu ba?”

Ya kai Musulmi! Ya kai wanda bashi ya yi wa nauyi! Ya wanda yake damuwa da ’yan lomomin abincin da zai rayu ga kansa da ’ya’yansa da matansa? Shin ka manta da Allah ne? Shin ka manta da komawa ga Allah ne? Ya wanda ba ya da aikin yi kuma ba ya da sana’a! Ka yawaita addu’a ga Allah. Ka ce: “Allahumma akfini bi halalika an haramika, wa aghanini bi fadailika an man siwaka.” Ma’ana: “Ya Ubangiji Ka wadantar da ni da halalinKa daga haraminKa, kuma ka wadatar da ni da falalarKa daga waninKa. Kuma ka ce: “Allahumma inni as’alukal huda wat tuka wal afafa wal ghina.” Ma’ana: “Ya Ubangiji! Lallai ne ni ina rokonKa shiriya da takawa da kamun kai da wadata.” Ka yi gaggawar haka, idan ka yi gaggawa Allah zai yi maka budi, kuma babu wanda ya kai Allah saurin karbar addu’a da rokon mai roko.

Ya ku muminai! Amma cikamakin wadannan kiraye-kiraye masu girma shi ne fadinSa Madaukaki: “Ya ku bayiNa! Iyaka wadannan ayyukanku ne Nake lissafo muku, sa’annan in sakanka muku a kansu. Don haka wanda duk ya samu alheri sai ya gode wa Allah. Wanda kuma ya samu akasin haka, to kada ya zargi kowa face kansa.”

Haka ne ya ku Musulmi! Lallai ne Ubangijinmu Mai girman Daraja – Yana kiyaye mana ayyukanmu Yana lissafo mana ayyukanmu da kanSa Madaukaki da mala’ikunsa masu tsaro wadanda Ya wakilta su a kanmu suke lazimtarmu dare da rana. “Lallai ne a kanku akwai wasu masu tsaro. Manya ne kuma marubuta. Suna sanin abin da kuke aikatawa.” (Al-Infidar: 10- 12).

Ka sani kai abin kai-kawo ne a kan iliminka, idan ka yi alheri ka huta, kuma ka yi burin abu mai falala. Idan kuma ka yi sharri ka yi ta fama da damuwa da firgici. Ku sani lallai ne rahamar Allah ta rigayi fushinSa, kuma afuwa ne mafi soyuwa a wurin Allah daga yin ukuba. Amma hakan yana samuwa ne ga wanda ya cancanci haka. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne Ni Mai gafara ne ga wanda ya tuba kuma ya yi aiki nagari, sannan ya nemi shiryuwa.” (daha: 82).

Ya Ubangiji! Muna rokon afuwarKa da gafararKa. Ya Ubangiji! Ka shiryar da mu a cikin wadanda Kake shiryarwa. Ka yi mana afuwa a cikin wadanda Kake yi wa afuwa. Ka jibince mu a cikin wadanda Kake jibinta! Ya Ubangiji! Lalli ne mu batattu ne, Ka shiryar da mu. Mu huntaye ne, Ka suturta mu, mu mayunwata ne, Ka ciyar da mu. Ya Ubangiji! Ka gyara zukatanmu da ayyukanmu. Ya Ubangiji! Ka sanya mu daga cikin masu tuba, kuma Ka sanya mu a cikin masu tsarkake ayyuka. Ya Ubangiji! Ka taimaki addininKa da LittafinKa da bayinKa salihai. Ya Ubangiji! Ka wadatar da mu da halalinKa daga barin haraminKa, kuma Ka wadatar da mu da falalarka da barin waninKa.

Ya Ubangiji! Ka biya bashin da yake kan duk wanda ake bi bashi, Ka warkar da marasa lafiyarmu da marasa lafiyar Musulmi. Ya Ubangiji! Ka gafarta mana da iyayenmu da duk wanda yake da hakki a kanmu. Ya Ubangjinmu! Ka ba mu sanyin ido game da matanmu da zuriyarmu, Ka sanya mu kasance shugabanni ga masu takawa. Ya Ubangiji Ka kyautata majibinta al’amarinmu da majibinta al’amuran Musulmi.

Ya Ubangiji! Ka mayar da mugun shirin masu mugun shiri na daga makiya Musulunci a cikin hancinsu, Ka taimaki rundunarmu a kansu. Ya Ubangiji! Ka tsare masu jihadi (kokari wajen yadawa da kare addininKa) a ko’ina suke a duniya. Ka dinke barakarsu, Ka tabbatar da duga-dugansu, Ka gyara tsakaninsu, Ka tsare su da tsarewarKa daga dukan abin ki. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabinmu Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa baki daya. Kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos