Kiraye-kirayen sauya fasalin kasa tamkar kiran a raba ta ne-Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kodayake kiraye-kirayen da wasu ke yi na sake fasalin kasar daidai ne amma sun bar kungiyoyin tsageru suna amfani da damar wajen kiran a raba kasar. Shugaban kasar sai ya yi gargadi wadanda suke goyon bayan raba kasar da cewa gwamnatinsa ba za ta taba kyale masu kiraye-kirayen ba. Shugaban […]
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kodayake kiraye-kirayen da wasu ke yi na sake fasalin kasar daidai ne amma sun bar kungiyoyin tsageru suna amfani da damar wajen kiran a raba kasar.
Shugaban kasar sai ya yi gargadi wadanda suke goyon bayan raba kasar da cewa gwamnatinsa ba za ta taba kyale masu kiraye-kirayen ba.
Shugaban kasar ya yi furucin ne a jawabin da ya yi wa ’yan kasar a ranar daya ga watan Oktoba, ranar da Najeriya ta samu ’yancin kanta daga turawan mulkin mallaka.
Ya ce a matsayinsa na karamin soja wanda ya sha gwagwarmaya a yakin basasan kasar wanda ya yi sandin mutuwar mutum miliyan biyu tare da asarar dukiyoyi masu yawa ba zai zura ido wasu bata-gari su kawo wa kasar matsala ba.