Kirifto DA ‘Mining’ A Tsakanin Matasan Arewa!

Akwai matasan Arewa masu harkar kirifto da ke riƙe coin na tsawon lokaci su manta da shi har sai ya kai wasu maƙudan kuɗaɗe su waiwaye shi

Kirifto DA ‘Mining’ A Tsakanin Matasan Arewa!

To da yake na shiga sabgar yanzu ina cikin shekarar farko, ina da tunanin wata rana matasanmu na Arewa za su faɗaɗa yadda suka fuskanci wannan lamari na kuɗaɗen kirifto har su samar da nasu na kansu.

Zan ɗan yi wata warwara dangane da hidimar a iyakar tawa fahimtar gare ta.

Akwai azuzuwan matasan da ke amfana da wannan harkar ta kirifto a Arewaci kamar yadda nake fahimta, daga ciki ana samun wasu da ake kira masu bumburutu, wato suna sayen duk wani ‘token’ da ake cikin haƙarsa tun kafin ya shiga wancan layi na ‘coin’ da ake hada-hadarsa a kasuwar kirifto.

Irin waɗannan wasu lokutan suna haɗawa da sayar da ‘gas fee’, wanda shi ma sana’ar sayar da ‘coin’ ne ga duk wanda ba zai iya sayensa da yawa ba, su ne suke sayar da shi cire-cire bayan sun saye shi da yawa sun tara.

Misalin masu bumburutu akwai Hafsat Ermum da Auwal Abdulƙadir Idris da sauransu birjik.

To sai kuma waɗanda su babu abin da suka fi mai da hankali kansa irin ‘trading’, wato a nemo wani ‘coin’ a duba yiwuwar tashin farashinsa, sai a sanya mashi kuɗi yadda za a sami riba a cikinsa idan ya tashi.

Irin wannan akan sami wasu da ke riƙe coin na tsawon lokaci su manta da shi har sai ya kai wasu maƙudan kuɗaɗe su waiwaye shi, hakan shi ake kira da ‘HODL’ (holding).

Masu ƙwarewa a wannan fannin na binciken ƙwaƙwaf a kan coin suna buɗe azuzuwa na koyar da duk wanda yake son ya iya saye da sayarwa saboda wannan harkar tana da samatsi ƙwarai.

A irin waɗannan azuzuwan ana sanya ‘signal’, wato idan sun yi bincike sun gano cewar wani coin zai yi daraja nan gaba, sai su kawo shi ga ’yan aji domin a saya a amfana.

Wasu lokutan ana iya samun riba, wani lokacin kuma a faɗi. Misalin waɗanda ke da azuzuwa akwai irin su Abubakar Tanko da Injiniya Auwal Zubair Tijjani da Ma’aroop Mustapha da sauransu da yawa.

A cikin waɗannan azuzuwan za a iske kuɗin rajistar shigar su har akwai wanda mutum ɗaya zai biya Naira miliyan ɗaya domin ya shiga.

To ban da wannan ajin akwai wanda ya fi shahara a tsakanin masu kirifto da ma waɗanda ba su yi, ba komai ba ne kuwa illa “Mining”.

Mining ɗin wannan da ake magana shi ne idan wasu gungun mutane ko kamfani ko haɗakas suna son ƙirƙirar coin, sai su nemi jama’a domin haƙo shi wannan coin ɗin ta hanyar amfani da wayoyi ko kwamfitoci, wannan ilmin mai zurfi ne ƙwarai ba zan iya zurfafawa a cikinsa ba domin yanzu nake fahimtarsa.

To bari mu duba wani abu game da su coins ɗin can da na ce ana haƙowa (Mining).

Wataƙil fahimtar wannan za ta sa mu gane shin matasan Arewa da ke mining za su iya ƙirƙirar nasu coin ɗin kamar yadda mutane a bayan fage suke son a yi, shin matasan nan suna samun wani abu ne da har suka riƙe harkar ba ji ba gani, matasan da ke mining “cima-zaune” ne kamar yadda wasu ke tsammani, da gaske ne yaudararsu ake yi ana cinye masu kuɗi, idan suna samun kuɗin me suke yi da su…?

A duniya kaf, akwai ƙiyasin da ke nuna masu tu’ammuli da kuɗaɗen kirifto sun kai miliyan ɗari biyar da tamanin.

‘Coins’ kuma da aka ƙirƙira baki ɗaya (waɗanda suka yi nasara da tasgaro da mutuwa…) ba su wuce guda 23,000 ba, a kansu ne wancan ƙiyasin mutanen suke ta wannan dab-dalar ba ji ba gani.

Ƙirƙirar sabon ‘coin’ ko project na ‘cryptocurrency’ yana buƙatar manyan kuɗaɗe waɗanda ba mamaki a ce kusan bajet ne na wata ƙasar a shekara guda, idan har ana son ya yi nasara ke nan yadda za a more shi.

Zan buga misali da wannan sabon ‘Notcoin’ da muka gama ‘mining’ nashi, a cikin kwana uku da aka ba da damar ajiye wasu ‘coins’ a ‘Binance’ domin kawai a mallake shi, kawo yanzu ana lissafin Dalar Amurka biliyan 13 ne (ba zan iya juya adadin zuwa Naira ba).

Wannan a ‘Binance’ kawai, ban da ‘OKX’ da su ma yau suka buɗe nasu ‘JumpStart’ ɗin.

Abin da nake son in haska shi ne, abu ne mai wahala a irin wannan ƙasar tamu a sami waɗanda za su kashe manyan kuɗaɗe ko su tallafa wa matasan da ke yunƙurin ganin sun cimma gaci a harkar.

Eh, tabbas ‘mining’ yana kawo alheri ga matasa, na san waɗanda a cikin masu ‘mining’ kowanne ya sami kuɗaɗen da mafarkinsa bai taɓa kai shi can ba.

Misali Sunusi Danjuma Ali lokacin da ‘ICE’ suka yi distribution nasu, duk da bai fito ya ce ga abin da ya samu ba, ina da yaƙinin ba za su gaza a miliyan 10 zuwa 15 ba, wannan a ‘project’ guda ɗaya ne da ya yi ‘mining.’

Haka Muhammad Sheka lokacin da aka yi ‘Airdrop’ na ‘GMRX’ ya bayyana sallamar da suka yi mashi ta doshi Naira miliyan goma.

Akwai matasa da yawan gaske waɗanda sun mallaki miliyan a yayin da ba su yi mafarkin za su same ta ba.

Ina da tabbacin ko siyasa da ke kawo wa matasa kuɗi idan sun yi wahala, ba a samu sosai kamar yadda ake samu a mining da ‘airdrop.’

Babban misali shi ne Rabiu Biyora yau idan aka ce ya zaɓa tsakanin ‘mining’ da siyasa, ba shakka zai jingine siyasa gefe ya doshi harkar ‘mining’ ɗin.

Akwai matasan da na sani sun gina gida sun yi aure sun sayi mota duk ta harkar mining ko airdrop.

Misali Mahadi Ahmad Daura ya tabbatar mani cewar kaso mafi tsoka na hidimar aurensa a shekarun baya da kuɗin mining ya yi.

Duk da haka, mafi akasarin waɗanda na sani suna ‘mining’ to Wallahi akwai wani ‘side hustle’ nasu. Misali Injiniya Adam Muhammad Mukhtar ya shahara a yin surfani, har yanzu da ya zama maloniya ta dalilin ‘mining’ bai manta da wannan sana’a ba.

Sanusi da na yi magana a farko ‘agent’ ne na MTN, yanzu kuma manomi ne kamar yadda ya bayyana da kansa.

Mu daina batu kan manyan ko shahararru, akwai Mahadi Ahmad da Auwal Abdulƙadir Idris duk sana’ar ɗinki suke yi.

Shi ‘crypto’ ba ya hana kowane irin aiki ko sana’a, ana dai ɗaukarsa kamar ribar ƙafa ne, kuma mafi akasarin masu yin sa to suna dabarar faɗaɗa jarin kasuwarsu, babban misali shi ne Crypto Love wanda hamshaƙin ɗan kasuwa ne a Kantin Kwari.

Abin da ya sa kirifto ko mining ya fi kowace sana’a shahara, saboda an fi yayata shi a kafafen Intanet, amma ba wai don masu yin sa ba su da sana’a ba.

Masu aikin ofis na yin ‘crypto’, ko shekaranjiya Wallahi na amsa kiran wani Dokta kuma malamin a makarantar gaba da sekondare yana tambaya ta wani abu game da ‘Notcoin.’

Na ji daɗi ƙwarai da gaske, na ƙara fahimtar abin ba iyakar namu ba ne matasa, na kowa da kowa ne, kamar dai ‘lockdown’ da aka yi, ya shafi kowa.

To amma duk da haka akwai matasa masu zama irin su Barista Abdul-Hadee Isah Ibraheem wanda yana kan gina sabon project na ‘cryptocurrency’ da ya sanya wa suna ‘SIC’ kuma In sha Allahu zai zama zakaran gwajin dafi, wanda zai ƙarasa sauya tunanin matasa, su ƙara zage dantse wajen faɗaɗawa da kutsawa a harkar.

Ta ɓangaren ilmantarwa a wannan fanni kuwa masana Blockchain da Cryptocurrency irin su Mahmud Muhammad Sardauna da Engr. Muhammad Sagir Muhammad sun duƙufa wajen koyar da matasa yadda za su mu’amalanci hidimar.

Wannan koyarwa kuwa ba ta tsaya a onlayin kawai ba, suna da makarantu a manyan jihohin Arewa kamar Kano da Bauchi da Adamawa inda matasa ke bin tsarin sayen fom da rajista kamar yadda manyan makarantu ke yi kafin su ɗauki ɗalibi.

Ban da wannan, akwai wani mashahurin matashi, Nasir I. Mahuta (ya rasu shekarun baya) da ya wallafa wani kandamin littafi da harshen Hausa, Sirrin Crypto.

Da a ce za a ɗauki crypto (ko ilmin Blockchain baki ɗaya) a matsayin cikakkiyar sana’a, manyan mutane masu ilmi ko wayewa ko kuɗi ko duk wani taimako da za a buƙata su kawo ɗauki a cikinta, ba shakka Arewa za su ƙara bunƙasa a harkar, duba da yadda matasa suka rungumi lamarin ka-in-da-na-in.

 

Hafiz Adamu Koza

Lambar Waya: 07060438556

Facebook: Hafiz Koza Adamu

Email: [email protected]

Abba ya yi tafiya yayin da rikici ya dabaibaye NNPP a Kano

Kotu ta hana EFCC kama tsohon minista kan taƙaddamar fili

Isra’ila ta ɗaiɗaita yara sama da 400,000 a Lebanon — UNICEF

Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso