Kiris ya rage rikicin limanci ya hana sallar Juma’a a babban masallacin Ogbomosho

Masu yunkurin hana sallar sun ce limamin masallacin ba dan garin ba ne

Kiris ya rage rikicin limanci ya hana sallar Juma’a a babban masallacin Ogbomosho

Babban masalacin garin Ogbomosho

An yi yunkurin dakatar da yin Sallah da tube rawanin Limamin babban Masallacin garin Ogbomosho da ke Jihar Oyo, Sheikh Teliat Yinus Oluwasina Ayilara, duk da yunkurin bai yi nasara ba.

Hakan dai ya biyo bayan samun wani sabani a tsakanin shugabannin al’ummar Musulmi a garin na Ogbomosho, lamarin ya haifar da yunkurin da bangare daya ya yi na rufe masallacin da kuma tube rawanin babban Limamin garin tare da dakatar da yin Sallar Juma’a ta yau.

Jagoran Musulman garin, wato Aare Musulmi na Ogbomosho, Alhaji Abdulganiy Atanda Owodunmi da Asoju Musulmi na Ogbomosho, Alhaji Minkaheel Yusuf da Balogun Musulmi na garin, Alhaji Abdulrazaq Bello, su ne suka jagoranci bangaren da ya rinka yekuwar ganin an tube babban Limamin.

Mutanen dai sun yi yunkurin ne saboda a cewarsu, Sheikh Teliat Yinus ba dan asalin garin ba ne.

Tun da safiyar Juma’a ce dai aka shawarci al’ummar Musulmi da suka saba yin Sallar Juma’a a babban masallacin da ke Oka’gbo, da su yi sallarsu a masallatai mafi kusa da su a dalilin rufe babban masallacin da aka shirya yi a ranar.

Sai dai Aminiya ta ji ta bakin daya daga cikin shugabannin Musulmin garin, Alhaji Bashiru Akanbi, wanda ya ce, “Dubban Musulmai maza da mata da suka saba yin sallar Juma’a ne suka halarci wannan masallaci a yau da Sheikh Teliat Yinus Oluwasina Ayilara ya jagorance mu wajen yin Sallah raka’a biyu ba tare da wata matsala ba.

“Shin ka taba jin inda aka rufe babban masallaci? Kuma Limamin wannan masallaci da suke so a tube masa rawani, marigayi Soun na Ogbomosho, Oba Jimoh Oyewunmi Ajagungbade ne ya nada masa rawani tun a shekara ta 2021, kuma sananne ne da yake da digirin digirgir a kan ilmin addinin Musulunci.”

Alhaji Bashiru Akanbi ya kara da cewa, “Su duka wadannan mutane 3 da suke so su haifar da abun da ba mu taba gani ba a tsakanin musulman Ogbomosho, ba sa zaune a garin, suna zaune ne a Legas. Saboda haka ka ga ba su san wainar da ake toyawa a cikin shi ba.”