Kiristocin Tudun Biri sun samu tallafin abincin Kirsimeti
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba da tallafin abincin Kirsimeti ga Kiristoci a Tudun Biri, kauyen da jirgin soja ya halaka mutane da yawa. Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne a ya kai kayan abinci domin taya Kiristocin bikin Kirsimeti. Aruwan ya kuma kasance cikin wadanda suka yi ibada a Cocin […]
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba da tallafin abincin Kirsimeti ga Kiristoci a Tudun Biri, kauyen da jirgin soja ya halaka mutane da yawa.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne a ya kai kayan abinci domin taya Kiristocin bikin Kirsimeti.
Aruwan ya kuma kasance cikin wadanda suka yi ibada a Cocin Nagarta Baptist da ke kauyen na Tudun Biri.
Aminiya ta fahinci akwai Kiristoci yara akalla uku da suka rasu a cikin mutanen da harin jirgin sojoji na ranar 3 ga Disamba dinnan ya rutsa da su a garin a lokacin da Musulmin garin ke bikin Maulidi.
- Kotun Ƙoli: Kwankwaso ya jagoranci addu’ar roƙa wa Abba nasara
- Ta antaya wa mijinta ruwan zafi saboda ya ki zuwa biki da ita
Da yake jawabi a cocin, Samuel Aruwan ya jaddada cewa harin da ya faru a ranar kuskure ne kuma suna fatan hakan ba zai sake faruwa ba a jihar da kasa baki daya.
“Mun zo ne domin taya mutanen garin Tudun Biri musamman Kiristocin garin murnar ranar Kirsimeti domin nuna musu cewa ba a mance da su ba, sannan muga cewa sun yi bikin Krsimeti lafiya cikin natsuwa.
“Saboda mun samu labarin wasu Kiristocin na nuna damuwar ganin kamar kika ba za su yi bikin ba saboda matsalar tsaro a yankin. Amma ga shi an yi bikin lafiya tare da Musulmin garin.
“Ganin Musulmi a cocin ya nuna yadda mutanen garin ke zaune lafiya da junansu, domin kusan komai a tare suke yi, wannan ya sa muka kawo musu kayan abinci domin taya su murnar wannan rana ta Kirsimeti” in ji shi.
Shi ma a jawabinsa Reverend Musa Saidu na cocin garin ya nuna farin cikinsa bisa wannan ziyara, inda ya roki gwamnati ta cika alkawuran da ta yi wa mutanen garin bayan wannan matsala ta auku.