Kirkiro Masarautu: Ganduje ya sake aika wa majalisa sabon kuduri
Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta sake aikawa da wani sabon kudiri ga majalisar dokokin jihar, domin kafa sabbin masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye. Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba, ya fitar da sanarwar a yau Litinin, wanda a yanzu haka majalisar ta karbi sabon kudurin a zauran majalisar. Majalisar zartarwa […]
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje
Kwanaki kadan kenan da wata kotu a Kano ta soke sabbin masarautun da aka kafa a baya, inda ta ce, ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka’ida ba.