Kirsimeti: Gwamnati ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa

Jigilar fasinjojin za a riƙa yinta cikin lumana a wurare biyar da suka haɗa da: Abuja zuwa Kaduna da Lagos zuwa Ibadan da Warri zuwa Itakpe da Portharcourt/Aba

Kirsimeti: Gwamnati ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa

A ranar Juma’a ne Gwamnatin Tarayya ta fara jigilar fasinjoji a jiragen ƙasa kyauta a faɗin ƙasar domin sauƙaƙa tsadar sufurin fasinjoji a faɗin ƙasar a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Muƙaddashin Manajan Daraktan Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC), Ben Iloanusi a lokacin da yake maraba da rukunin farko na fasinjojin da suka isa tashar jirgin ƙasa ta Kubwa da ke Abuja daga Rigasa, ya ce Hukumar ta nuna damuwa kan yadda za a kare lafiyar fasinjoji a ranar farko.

Sai dai ya ce Hukumar na ɗaukar matakan magance matsalolin tsaro da fasinjojin za su iya fuskanta.

Da yake jawabi, ya kuma bayyana cewa “jigilar fasinjojin kyauta zai ɗauki fasinjoji 20,000 a kullum domin gwamnatin tarayya ta yi ƙiyasin yin jigilar kyauta ga fasinjoji 340,000 kafin wa’adin jigilar ya ƙare a makon farko na watan Janairu.”

Ya ƙara da cewa, jigilar fasinjojin za a riƙa yinta cikin lumana a wurare biyar da suka haɗa da: Abuja zuwa Kaduna da Lagos zuwa Ibadan da Warri zuwa Itakpe da Portharcourt/Aba da kuma Lagos Mass Transit.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025