Kirsimeti: NSCDC Ta Girke Jami’ai 780 A Gombe

Hukumar Sibil Difens ta girke jami’anta 780 domin bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara a Gombe

Kirsimeti: NSCDC Ta Girke Jami’ai 780 A Gombe

Dakarun Rundunar ta Musamman ta mata zalla da NSCDC ta kafa. (Hoto: @raufaregbesola).

A kokarinta na kare rayuka da dukiyoyi Gombe, Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta girke jami’ai 780 domin sintiri a Jihar Gombe a lokacin bukukuwan kirsimeti da sabuwar Shekara.

Kwamandan hukumar a jihar, Muhammad Bello Mu’azu, ne ya sanar da hakan, yana mai umurtar Kwamandojin Yankin da na Kananan hukumomi da sauransu cewa su tabbatar sun tura isassun jami’ai a lungu da sakon jihar.

A cewar sanarwar, za a tura jami’an ne a wuraren ibada da kasuwanni da tashohin mota da kuma wuraren shakatawa.

Sannan sai ya bukaci jama’a da su yi bukukuwan a tsanake wajen kiyaye doka da oda domin jami’ansa za su yi aikinsu ba sani, ba sabo.

A cewarsa, za su tabbatar da ganin sun tsare rayuka da dukiyoyi yadda ya dace kafin lokacin kirsimeti da kuma Sabuwar Shekara.