Kirsimeti: NSCDC ta Tura jami’ai 850 don tabbatar da tsaro a Gombe

Hukumar ta nemi haɗin kan jama’ar jihar don gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali.

Kirsimeti: NSCDC ta Tura jami’ai 850 don tabbatar da tsaro a Gombe

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), ta tura jami’ai 850 wurare daban-daban a Jihar Gombe domin tabbatar da tsaro yayin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Kwamandan hukumar a jihar, Gyama Gyawiya ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar.

Ya ce an ɗauki wannan matakin ne don kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar, tare da tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan.

Sanarwar ta ce jami’an da aka tura za su mayar da hankali kan tsaro a ƙananan hukumomi 11 na jihar, musamman a wuraren ibada, tashoshin mota, wuraren shaƙatawa, da muhimman kadarorin gwamnati da na masu zaman kansu.

Bugu da ƙari, an haɗa jami’an tsaron da ke da ƙwarewa daga sassa daban-daban na hukumar, ciki har da SWAT, CTU, Agro Rangers, Mining Marshal, da sashen bincike.

Gyawiya, ya yi kira ga jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ga hukumar ko sauran jami’an tsaro.

Hukumar ta ce an yi haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan, tare da ɗaukar matakai na musamman.

NSCDC, ta kuma buƙaci jama’ar Gombe su bayar da haɗin kai domin yin bukukuwan cikin kwanciyar hankali.