Kirsimeti: Sanata Uba Sani ya tallafawa marasa galihu da abinci
Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Uba Sani ya rabawa marasa galihu abinci domin murnar bikin Kiristimiti a mazabarsa. Ya kuma bukaci Kiristoci da su yi amfani da wannan rana wajen yada kauna da zaman lafiya a cikin al’umma. Sanata Uba Sani ya kuma yi kira da masu kudi da su rika tunawa da […]

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Uba Sani ya rabawa marasa galihu abinci domin murnar bikin Kiristimiti a mazabarsa.
Ya kuma bukaci Kiristoci da su yi amfani da wannan rana wajen yada kauna da zaman lafiya a cikin al’umma.
Sanata Uba Sani ya kuma yi kira da masu kudi da su rika tunawa da talakawa da ke cikinsu ta hanyar tallafa masu.
“Dole ne mu rika taimakawa marasa galihu dake cikin mu domin mu faranta masu rai. Yin hakan zai yi daidai da koyarwar Annanbi Isa.”