Kirsimeti: Zulum Ya Bayar Da Umarnin Biyan Ma’aikatan Borno Albashin Disamba

Matakin na nufin bai wa ma’aikata da ’yan fansho damar samun walwala da isassun kuɗi don shirya bukukuwansu ba tare da wata damuwa ba.

Kirsimeti: Zulum Ya Bayar Da Umarnin Biyan Ma’aikatan Borno Albashin Disamba

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya umarci a biya ma’aikata da ’yan fansho albashin watan Disamba domin su samu sauƙin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara cikin kwanciyar hankali.

Sanarwar ta fito daga kakakin gwamnan, Dauda Iliya, wanda ya fitar da bayanin ga manema labarai a Maiduguri.

A cewar Iliya, wannan mataki na nufin bai wa ma’aikata da ’yan fansho damar samun walwala da isassun kuɗi don shirya bukukuwansu ba tare da wata damuwa ba.

Ya ƙara da cewa Gwamna Zulum ya kasance cikin shugabannin farko da suka aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 a Najeriya.

Hakazalika, Iliya ya bayyana cewa biyan albashin da wuri yana ƙarfafa haɗin kai a tsakanin ma’aikata da kuma al’ummar jihar baki ɗaya.

Ya ce: “Gwamna Zulum ya bayar da umarni cewa kowa ya ji daɗin gudanar da bukukuwansa, ba tare da la’akari da addininsa ba, domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a jihar.”

Ya kuma jaddada cewa Jihar Borno na ɗaya daga cikin jihohin da al’ummarsu ke rayuwa cikin fahimtar juna duk da bambance-bambancen addini da al’adu.

Da yake gabatar da kasafin kuɗi na Naira biliyan 585 a gaban majalisar dokoki, Gwamna Zulum ya yi alƙawarin inganta jin daɗin ma’aikata duk da matsalolin tattalin arziƙi da ake fuskanta.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙara inganta tsarin biyan albashi tare da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 72,000, da kuma biyan haƙƙoƙin ma’aikatan da suka rasu.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra