Kisa a Binuwai: Fataken shanu za su daina kai shanu Kudu

Fataken Shanu daga shiyyar Arewa maso Gabas sun yi barzanar shiga yajin kai shanu Kudu sakamakon kashe wakilansu lokacin da suke wucewa ta Jihar Binuwai, inda suka ayyana zaman makoki na kwana uku.Fataken shanun sun kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta bi musu kadin kashe wakilansu takwas da aka yi aka kone musu shanu sama da […]

Kisa a Binuwai: Fataken shanu za su daina kai shanu Kudu

Fataken Shanu daga shiyyar Arewa maso Gabas sun yi barzanar shiga yajin kai shanu Kudu sakamakon kashe wakilansu lokacin da suke wucewa ta Jihar Binuwai, inda suka ayyana zaman makoki na kwana uku.
Fataken shanun sun kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta bi musu kadin kashe wakilansu takwas da aka yi aka kone musu shanu sama da 50 da mota tirela yayin da ’yan kabilar Tibi suka rika tsare hanya da sunan daukar fansa kan rikicinsu da Fulani a karamar Hukumar Aliade da ke cikin Jihar Binuwai makon jiya.
Shugaban Fataken Shanu na Jihar Gombe, Alhaji Yahuza Yusuf ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da suka kira a Bauchi, inda ya yi zargin cewa Tibi sun kashe musu mutane takwas daga Jihar Gombe a Aliade a hanyarsu ta zuwa Aba, lokacin da suka kafa shinge a garin Kuyanga.
Alhaji Yahuza Yusuf, wanda ya nemi gwamnatin Binuwai ta biya su diyya ko su shiga yajin aiki, ya ce su a Jihar Gombe sun dakatar da safarar da suke yi na akalla tirela 25 zuwa 50 na shanu ko kayan abinci zuwa Kudancin kasar nan har sai an bi musu hakkinsu.
Ya ce tare da DPO na Aliade suka dauko gawarwakin mutum uku suka yi musu jana’iza, yayin da mutum biyu aka jefa gawarsu a cikin motar shannun tana cin wuta, su kuma mutum uku har yanzu ba a san inda gawarwakinsu suke ba.
Ya ce da farko idan an buga wayoyinsu sai a dauka a ce ‘mu ne Tibi, mun kashe su ku ma idan kuna son mutuwa ku zo’, daga baya sai aka kashe wayoyin.
Ya ce lokacin da za su je garin Aliade sai da suka nemi rakiyar jami’an tsaro zuwa Makurdi ganin yadda ake ta kashe Hausawa da Fulani ana kone musu dukiya a kan hanya.
Shugaban kungiyar direbobin manyan motoci na Jihar Gombe, Malam Adamu Juma ya ce bayan sun dauki gawarwakin zuwa makabarta duk da akwai jami’an tsaro, an yi ta kai musu hari da kyar suka gama jana’izar suka tafi ba tare da gwamnatin jihar ta tallafa musu ba.
Ya ce kisan gilla da kone dukiya da kabilar Tibi ke yi wa Hausawa da Fulani fataken shanu da kayan abinci da sunan daukar fansa lamarin ne da ko kare ba zai ci ba.