Kisan al’umma a Jihar Zamfara, kukan kurciya…
Shakka babu halin rashin zaman lafiyar da talakawan Jihar Zamfara suka samu kansu ciki, yana neman ya gagari kundila.Abin da ban mamaki ganin yadda mahara suke afka wa kauyukan jiharmu ta Zamfara, suna kashe wanda bai da sauran kwana, su lahanta mai rabon wahala, wani kuma su yi mai kat tare da yi wa mata […]
Shakka babu halin rashin zaman lafiyar da talakawan Jihar Zamfara suka samu kansu ciki, yana neman ya gagari kundila.
Abin da ban mamaki ganin yadda mahara suke afka wa kauyukan jiharmu ta Zamfara, suna kashe wanda bai da sauran kwana, su lahanta mai rabon wahala, wani kuma su yi mai kat tare da yi wa mata fyade!
Haba, wannan masifa da me ta yi kama? Mu dai mun san wannan matsalar ba ta fi karfin gwamnatocinmu ba amma
muna iya cewa ta fi karfin jami’an tsaronmu, domin maganar gaskiya wadannan maharan sun fi jami’an tsaron kasata makaman kirki. Baya ga haka, ba wani tallafin kirki da ake bai wa iyalin jami’in tsaron da suke rasa rayukansu a fagen daga.
Daga karshe nake jan hankalin shuwagabanninmu da su tashi tsaye, su magance wannan matsala tun kamin wankin hula ya kai mu dare. Domin duk lokacin da talakan Najeriya zuciyarsa ta bushe, to fa abin da ya faru a
Masar da Tunusiya da Libiya ba wai ya fi karfin ya faru a Najeriya ba ne. Duk da cewa shuwagabannin sun hore mu da yunwa da jahilci, wadanda su ne manyan kangunan da ke hana talaka sanin kowa ye shi a sararin subhana. Kukan kurciya dai jawabi ne amma ga mai hankali.
Abdulmalik ya aiko daga Gusau Jihar Zamfara (08069807496)