Kisan al’ummar Zamfara a kan idanun shugabanninmu na Arewa

Manzon Allah (SAW) allallahu ya ce, karshen duniya idan ya gabato  kisa zai yawaita, tashin hankali zai yawaita, har ta kai matsayin wanda yake kisan bai san dalilin kisan ba, shi ma wanda ake kashe bai san me ya aikata aka kashe shi ba. Mun ji mun kuma yi da’a gare ka Ya Rasulullah! Ba […]

Kisan al’ummar Zamfara a kan idanun shugabanninmu na Arewa
Kisan al’ummar Zamfara a kan idanun shugabanninmu na Arewa

Manzon Allah (SAW) allallahu ya ce, karshen duniya idan ya gabato  kisa zai yawaita, tashin hankali zai yawaita, har ta kai matsayin wanda yake kisan bai san dalilin kisan ba, shi ma wanda ake kashe bai san me ya aikata aka kashe shi ba. Mun ji mun kuma yi da’a gare ka Ya Rasulullah! Ba shakka a halin da ake ciki yanzu na kashe-kashe da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa sun yawaita a Arewacin Najeriya da sauran wurare da dama.

Wannan duk yana faruwa ne bisa kaddarawar Ubangiji (SWT)da kuma sakaci na shugabanninmu. Don haka, yana da kyau a lokacin da mutane ke cikin tsananin firgici da damuwa, su kame harsunansu daga furta kalaman da za su kasance masu yin nadama a Ranar Alkiyama.

Mu yi hakuri mu mai da al’amuranmu ga Allah, mu yi gaskiya, mu ji tsoron Allah gwargwadan iko, kada mu yi shirka, kada mu zargi Allah a kan abubuwan da suke faruwa gare mu. Mu sani cewa Allah Mai ji ne kuma Mai gani ne. Allah da kanSa Ya ce, “Ka yi bushara ga masu hakuri,” da juriya a lokacin tsanani. Ba shakka abin da yake faruwa gare mu ya wuce duk yadda muke kaddara shi, mu kyautata zato ga Allah, mu ji tsoron Allah a maganganunmu da ayyukanmu. Allah Ya hana wa kanSa zalunci, Ya ce kuma sai ya sakawa duk wanda aka zalunta, koda kuwa wanda aka zalunta bai ce Allah Ya saka masa ba. Ya shugabanninmu na Arewa da sauran ’yan uwa! Ku sani ko daidai da magana idan ka zalunci wani Allah ba zai yafe ba matukar ba wanda aka zalunta din ba ne ya yafe. Mu ji tsoron Allah, mu kiyaye harsunanmu wajen furta kalaman da za su zama nadama gare mu ranar da nadamar ba za ta amfana wa bawa  komai ba, wannan ke nan.

Ya ku shugabanninmu na Arewa tun daga kan tsofaffin shugabannin kasa da mataimakansu da sarakuna da manyan jami’an tsaronmu manyan ’yan siyasa da masu fada-a-ji da manyan attajiranmu da manyan malaman addini dana zamani da sauran kasa-kasa talakawan da ake jagoranta! Na san cewa ba ku manta da irin masifar da muka baro a baya ba ta bala’in Boko Haram wanda ’yan uwanmu da ke Arewa maso Gabas suka gani dama wasu sassan kasar nan ciki har da Jihar Kano inda aka shiga tashin hankalin da ba a tava shiga ba tun kafuwar jihar, kuma har yanzu akwai vurvushinsu jefi- jafi amma ba kamar yadda gwamnatin baya ta yi wasa da rayukan jama’a ba, har muke ganin waccan gwamnatin tana sha’awar wadannan kashe-kashe da ake a Arewa maso Gabas da sauran yankunan Arewa. Aka mayar da rayukan mutane ba a bakin komai ba, a lokacin aka rika yin gudun yada-kanen wani uba ya gudu ya bar matarsa ga ’ya’ya, uwa ta gudu ta bar ’ya’yanta duk dukiyar mutum haka zai tsallake ta ya gudu shi ke nan sun zama marayu. Amma saboda da mantuwa shugabanni duk kun manta ke nan ba ku gudun abin da ya faru da jihohin Borno da Yobe da Adamawa da wasu sassa na kasar nan ya faru a wannan yanki na jihohin Zamfara  da Katsina da Kaduna wanda kusan shekara guda ana yin abu daya har yau an gaza kawo karshen kashe-kashe da satar mutane a wannan yankin? Shi ke nan haka za mu zauna ba mu da tsari an faro kashe mu daga farkon Arewa an kakaba mana Boko Haram shi ne za a kare a karshen Arewa ana kashe mutane tare da sace su ana neman kudin fansa. Shugabanninmu yanzu kuna ji kuna gani idan har ba so ake a mayar da talakawan Arewa tamkar awakin layya ba muna ganin abin nan kullum zubar da jini ake yi a Jihar Zamfara ga satar jama’a kan titin Kaduna zuwa Abuja. Gaskiyar magana ya kamata ku ce wani abu a kai tare da daukar hanyar gyarawa in dai ba so ake mu koma tamkar Somaliya ko Libya da Zirin Gaza ba, Allah Ya kare mu.

Mai kawo karshen wannan iftila’in da ke faruwa a Zamfara ita ce Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Baba Buhari da sauran makusantansa da Allah ya dora wa alhakin shugabancin al’ummar kasa ku tuna cewa kare lafiya da dukiya suna wuyan Baba ne kuma wannan gwamnatin daya daga cikin abin da ya sa al’ummar kasa suka ce lailai sai an kawo CHANJI shi ne rashin tsaro da ya jefa firgici da tsoro a cikin zukatanmu kuma cikin ikon Allah muka yi kokari, masu rubutu na yi, masu shiga rediyo na yi masu yi a majalisun zaman mutane na yi, da sauran hanyoyin wayar wa al’ummar kasa kai a birni da kauyuka har sai da aka ci galabar PDP a kasar nan, aka tabbatar da kafuwar wannan gwamnati mai aldalci a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015, kuma yanzu an tafi Matakin Gaba #NedtLevel. Don haka tunin da zan yi wa Shugaban Kasa shi ne irin wannan ta’addacin da ake yi a Zamfara ka tuna kai kanka an yi yunkurin kashe ka a Kaduna Allah bai nufa ba. To yanzu duk dan kasa ya zuba ido da sauraron ka yi magana ko ka bayar da umarni kan matakin da ya dace ga Zamfara.

Maganar gaskiya idan ana son kawo karshen wannan ta’addancin na kisa da garkuwa da mutane a Jihar Zamfara da sauransu, ya zama wajibi Shugaba Buhari da jami’an tsaro da gwamnatin jihar da shugabannin Arewa tun daga kan sarakuna da manyan malaman addinin Musulunci da na boko da manyan masu fada- a-ji na jihar da masu ruwa-da-tsaki, su tsoma baki don kawo karshen wannan ta’asa tun kafin abin ya ta’azzara ya gagari kwandila. Wato ya zamo su kansu jami’an tsaro da suke da ikon kare lafiya da dukiyoyin al’umma  a shiga kashe su a irin wannan harkar ta ta’addanci, kamar yadda Boko Haram ta ishe mu darasi.

Mai girma Shugaban Kasa Buhari da sauran makusantanka kada fa ku manta cewa, nasararka nasarar mu ce mu ’yan Arewa Musulmi kuma Hausawa da Fulani. Haka gazawarka gazawarmu ce ko mun ki ko mun so, duk irin zagin da ake yi masa kullum ba fa Buhari ake zagi ba mu din ne da muka ce a zave shi ake zagi.

Don haka muna da hakkin mu fada a gyara muddin aka yi kuskure, saboda muna fata mu hadu da Allah lami lafiya a kan irin rayukan da ake kashewa  ko ake sacewa a yankinmu na Arewa. Kuma mu din ne kirjin biki wajan tallafawa a kafa wannan gwamnati tamu mai albarka. Kamar yadda kowa ya sani mulki shi ne karshen karfi na yin gyara ko varna, saboda haka bai kamata a ce al’ummar Jihar Zamfara da sauran inda suke da matsalar tsaro a bar su kara-zube ba. Duk wata amanarmu, mun yarda muka nema mata ahlin da ya dace da ita, musamman amanar rayukanmu da lafiyarmu da dukiyarmu da mutuncinmu da adininmu. Kada mu zo duniya a banza, mu rayu a banza, mu mutu a banza.

’Yan uwana ’yan Najeriya! Babu abin da Allah zai canja mama sai mu ma mun canja, mun daina sava wa Allah. Idan mutum ya sava wa Allah ya yarda ya sava maSa, sai Allah Ya biya masa bukata. Tunda Allah Ta’ala Ya tsara yadda za a yi shari’a ta adalci, ya tanadi a yi kotu da alkalai da kurkuku da ’yan sanda tun a nan duniya kafin a je Lahira a yi hukunci karshen, wajibi ne mu yi cikakken amfani da wannan dama a hukunta duk wanda ya sava, kamar yadda Allah Ya yi umarni. Kowa ya san ba shi ne ya halicci kansa ba, Allah Ta’ala Shi ne Ya halicci kowa da komai, Ya kuma tsara yadda Yake so mu rayu. Saboda haka Allah shi ne Gwani ba wani ba. Mu yi riko da igiyar Allah, mu daina rarrabuwa. Mu kiyaye dokokinSa da umarninSa, mu yi abin da Ya ce, mu bar abin da Ya hane mu, shi ne zaman lafiyarmu. Allah Ya tsara mana yadda za mu rayu da juna, komai irin bambancin da ke tsakaninmu, na addini, kabila, vangare, ko launin fata, illa mu bi wannan tsari da Allah Ya shimfida mana.

A karshe shugabanninmu kada fa sun manta cewa da yawansu fa ’ya’yan talakawa ne talak da suke rike da madafun iko a kasar nan haka duk wanda yake amfani da mulki yana aikata zalunci da firgici a zukatan al’umma, ya tuna magana ce ta lokaci ga mu ga Allah! Duk wanda da sa hannunsa wajen kirkirar ta’addanci a wasu sassan kasar nan ake zubar da jinin al’umma tabbas ba ya jin tsoron Allah, ba ya jin kunyar mutane, Allah Ya tona asirinsa saboda bai kamata a ji tsoronsa ba, balle ma a ji kunyarsa. Duk abin da yake tinkaho da shi kuma Allah Ya fi shi, ko wane ne shi, kuma ko dan wane ne.

Allah Ya zaunar mana da jihohinmu da kasarmu lafiya Ya sa komai ya zama tarihi. Kuma ina FATAN WANNAN SAKON ZAI KARADE KASAR NAN SANNAN YA ISA WURIN DA YA DACE YA JE. Kamar lokacin da na tura irin wannan sakon a shekarun baya lokacin da wadansu maciya amana suka kai wa Shugaba Buhari hari a Kaduna Allah Ya tsallakar da shi daga kaidinsu har na ba wa rubutun suna “Wa yake son kashe Buhari?”

Anas Saminu Ja’en

08188742103

[email protected]