Kisan Apo: ‘An hana mu ganawa da wadanda ake tsare da su’
Fiye da mako hudu bayan kashe mutum tara da jami’an tsaro suka yi a wani gida da ba a kammala ba a Unguwar ’Yan majalisa da ke Apo a Abuja, an hana wasu ’yan Majalisar Tarayya da ’yan uwan wasu da ke tsare daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ganinsu.’Yan Majalisar Tarayyar sun […]
Fiye da mako hudu bayan kashe mutum tara da jami’an tsaro suka yi a wani gida da ba a kammala ba a Unguwar ’Yan majalisa da ke Apo a Abuja, an hana wasu ’yan Majalisar Tarayya da ’yan uwan wasu da ke tsare daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ganinsu.
’Yan Majalisar Tarayyar sun koka kan yadda duk da zuwa da kansu domin ganawa da wadanda ake tsare da su, jami’an tsaro sun hana su ganinsu, inda suka la’anci gazawar jami’an tsaron na bayyana sunayen wadanda suka ce suna tsare da su.
Wasu ’yan uwan wadanda ake tsare da su, sun shaida wa Sashin Hausa na gidan rediyon BBC Landan cewa suna tsoro kan bin da zai samu wadanda ake tsare da su din, inda suka ce ba su da alaka da Boko Haram.
Da yake magana da Aminiya ta waya wani dan Majalisar Tarayya Bilyaminu Yusuf Shinkafi (PDP Zamfara), ya ce duk kokarin da wasu ’yan majalisar sukai domin ganin wadanda ake tsare da su ya ci tura, inda ya kara da cewa, ba zai iya cewa ga inda suke ba. “Mun yi ta kokarin gano wadanda aka ce ana tsare da su, ba tare da mun samu nasara ba. Ko kafin mu tafi hutun Sallah, Majalisar Dattawa ta yi nisa kan lamarin. Hakika mun damu kan halin da ake ciki, kuma mun san irin kuncin da iyalan wadanda aka tsaren suke ciki,” inji shi.
Bilyaminu ya ce, koma mene ne ake zarginsu da shi, suna da ’yancin ganawa da iyalansu, kuma suna da ’yancin samun kariyar lauyoyi ko kare su kamar yadda yake kunshe a cikin tsarin mulki.
“Ba mu kadai muke aiki ba; muna aiki da wasu lauyoyi da sauran masu kare hakkin dan Adam domin ganin an yi adalci a kan lamarin. Wasu daga cikin wadanda aka yi wa rauni an sallame su daga asibiti,” inji shi.
Shi kuwa Sakataren kungiyar ’Yan Kasuwar Zamani ta Garki wanda shi ma dan Jihar Zamfara ne, Murtala Abubakar Moriki, ya ce mutum 13 ne daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su suka bace, kuma har yanzu ba su san inda suke ba, domin jami’an tsaron ba su bayyana musu komai ba.
Wani dan Majalisar Tarayyar Alhaji Ashiru Tukur Idris ya shaida wa Sashin Hausa na rediyon BBC Landan a ranar Talata cewa, duk yunkurin da suka yi an hana su ganawa da wadanda ake tsare da su.