Kisan dalibai 30 a Yobe Na fito fitsari na gamu da makasan -dalibi
Wani dalibin makarantar sakandaren gwamnati ta Mamudo da ke karamar hukumar Potiskum a jihar Yobe da ‘yan bindiga suka kashe mutum 30, a makon da ya gabata, shi kuma ya sha da kyar, mai suna Adamu Isa ya ce lokacin da ‘yan bindigan suka zo makarantar tasu da tsakar daren ranar ta asabar ya fito […]

Wani dalibin makarantar sakandaren gwamnati ta Mamudo da ke karamar hukumar Potiskum a jihar Yobe da ‘yan bindiga suka kashe mutum 30, a makon da ya gabata, shi kuma ya sha da kyar, mai suna Adamu Isa ya ce lokacin da ‘yan bindigan suka zo makarantar tasu da tsakar daren ranar ta asabar ya fito yin fitsari ne ya hange su. A cikin wannan hargitsi na makarantar tasu, dalibin dan kimanin shekaru 17 ya hangi kwambar wadansu mutanen da ba zai iya gane su ba saboda duhun dare sun nufo makwancinsu, kasancewar bai saba ganin hakan ba sai ya labe a bayan wani gini, to daga bisani sai ya ji karar harbe-harben bindiga, sai ya sadada ya fita wajen makarantar a guje.
Wannan dalibii ya kara da cewa, daga bisani sai ya ji harbe-harben bindigogi ta kowace kusurwar makarantar tare da jin kururuwar ‘yan uwansa dalibai, a lokacin shi ya kai ga shiga garin Mamudo. “Iya abin da na sani ke nan,’’ a cewar dalibin.
daya daga cikin malaman makarantar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ya ga tashin hankali kuru-kuru a wannnan ranar da al’amarin ya faru.
Ya bayyana wa Aminiya cewa yana gidansa aka sanar da shi cewa ‘yan bindiga sun harbe daliban makarantarsa. “A wannan rana na ga abin bakin ciki da ban mamaki, a duniya ban taba tunani ko hasashen irin wannan rashin imanin zai iya faruwa ba.”
Ya kara da cewa, “Isata makarantar ke da wuya sai na tarar da gawawwakin yara birjik a kasa, gawawwaki uku an kone su, sauran yara ashirin kuma suna kwance cikin jini. Mutanen gari suka taimaka aka lullube gawawwakin da tabarmi da zannuwan gadajensu kafin Jami’an tsaro suka kwashe su zuwa Babban Asibin Potiskum.”
Haka kuma malaminya koka kwarai a kan yadda gwamnati ba ta dauki mataki ba har mummunan al’amarin ya kasance. “Akalla makonni biyar da suka wuce, wadansu mutane suka zo suka kashe Nuhu Datam, kama suka ce za su dawo su kone makarantar, shugaban makarantar ya kwashe iyalinsa daga makaranta, malaman makarantar duk sun gudu, ban da Malam Ibrahim Tikau da kaddarara ta afka wa bayan ya kama gidan haya a Potiskum, yana kokarin tarewa.”
Ya bayyana wa Aminiya cewa, babbar hanya da za a bi domin magance faruwar wannan a’amari shi ne ta hanyar zagaye makarantar da Katanga tare kuma da kawo jami’an tsaro da za su kula da rayuwar daliban
Ya kuma shawarci gwamnati ta yi tunani mai ma’ana wajen ganin an maido da sabis din wayar hannu, domin sau da yawa mutane kan ga ‘yan ta’addar amma babu hanyar sadarwa da za su kira jami’an tsaro.
Aminiya ta hadu da wani malamin makarantar a asibitin garin Potiskum wanda ya je don yin dubiya amma ya yi rokon kada a bayyana sunansa saboda matakan tsaro, ya yi karin haske da cewa,alal hakika wadannan ‘yan bindiga yadda suka shiryo suka afka wa makarantar tasu abin kamar shiryayya ce, ko kuma dama can sun dade suna kulla makircin aiwatar da wannan aika-aika tasu, don a tsanake suka shigo ba tare da taraddadin ko za su samu martani daga jami’an tsaron da ke kula da dokar ta baci a jahar ba, wato JTF, don kuwa su ma da kansu malaman makarantar Allah (SWT) ne kawai Ya tserar da su, don kadan ya rage su ma ‘yan bindigan su afka musu, illa dai malami daya da wannan bala’i ya rutsa da shi.
Malamin ya kara da cewa, ana cikin wannn harbe-harbe ne suka samu suka tsere daga harabar makarantar inda suka samu mafaka a wani wurin har yayin da kura ta lafa, suka fito suka tarar da irin barnar da ‘yan bindigan suka aiwatar a kan adlibansu da kuma wadansu bangarori na gine-ginen makarantar da suka kone su kurmus.
Shi ma Muhammadu Sani, wani dalibin aji biyu a makarantar da ya tsira da harbin bindiga a kirji, ya bayyana wa Aminiya cewa, suna kwance a daki da misalin karfe 3:30 na safe, “Sai ‘yan bindiga suka watsa mana man fetur, bude idan na ke da wuya sai na ga duk sun kewaye mu. Daga karshe suka sanya muka kwanta a kasa, haka suka rika tantance mu suna ware balagaggu da kuma wadanda ba su balaga ba. Mu da suka leka gabanmu da hammatarmu suka ga gashi suka harbe mu. Allah kadai Ya sa ina da sauran kwana ban mutu ba.”
Haka kuma ya bayyana wa Aminiya cewa, wadansu daga cikinsu an kulle su cikin offishin shugaban makarantar wanda a nan ne suka tantace wadansu daliban kuma suka kona wadansunsu, amma ya ce bai san yawan yaran da aka kashe ba. “Mu dai a UBE house mun kai kusan Ashirin, amma ban san yara nawa aka kashe a Senior section ba.”
Ita kuwa kungiyar malaman makaranta ta kasa yaba wa gwamnatin jahar Yob eta yi kan matakin da ta dauka na rufe duk makarantun sakandaren jahar har zuwa sabuwar shekarar karatu da za ta fara a watan Satumba mai zuwa sakamakon hare -haren da ‘yan bindiga ke kai wa makarantun wanda ke haifar da rasa rayukan dalibai da malamai, kamar yadda ya faru a makarantar sakandaren kwana da ke garin Mamudo cikin karamar hukumar Potiskum da ‘yan bindiga suka hallaka dalibai sama da 30 da kuma malami guda.
Shugaban kungiyar malamai ta kasa (NUT) reshen jihar Yobe Malam Lawan Ibrahim ne ya yi wannan yabon a jawabinsasa ga manema labarai jim kadan da bada wannan umarni na rufe makarantun da gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ya yi.
Shugaban ya kara da cewa, kungiyar tasu ta NUT tana kuma shawartar gwamnatin jihar ta yi kokarin rufe sauran makarantun firamare da kananan makarantun sakandaren jeka ka dawo da ke jihar domin rigakafin abin da ka iya zuwa ya dawo.
Malam Lawan Ibrahim ya kuma nuna alhininsa gami da jajanta wa dukkan iyaye da iyalen malaman da wannan al’amarin ya rutsa da danginsu, ya kuma yi fatan Allah( SWT) Ya kiyaye sake faruwar irin hakan.
Shi ma mai taimakawa na musamman ga gwamna Gaidam kan harkokin ilmi Alhaji Mai Aliyu Biriri ya nuna rashin jin dadinsa matuka bisa faruwar wannan hari na ‘yan bindiga,ya ce wannan abu babban abin ki ne, ya yi fatan Allah( SWT) Ya kawar da sake faruwar irin wannan abu domin babbar asara ne ga kasa.
A karshen mako ne dai wadansu ‘yan bindiga da ba a san su ba suka kai wani mummunan hari kan makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Mamudo cikin karamar hukumar Fune a jihar Yobe inda suka hallaka sama da dalibai 30 da malaminsu daya tare da barin wadansu daliban da munanan raunuka da suka samu a sanadiyyar harbin bindiga ko kuma yayin kokarin tsere wa harin.
Wata majiya a garin na Mamudo ta shaida wa Aminiya cewa, da misalin karfe ukun daren ranar asabar ne maharan suka kai wannan mummunan farmaki nasu a yayin da daliban ke kwance a dakunansu.
Majiyar ta kara da cewa, lokacin da karan harbe-harben ‘yan bindigar ya yawaita shi ne daliban suka rika farkawa a firgice suna yunkurin fita da gudu ba da shirinsu ba, hakan ne ya bada dama ga’yan bindigan suka rika harbe duk wanda suka gani tare da rutsa wassunsu a dakunansu suna cinna musu wuta tare da tare kofofin dakunan ta yadda duk wanda ya fito sai kawai su bindige shi.
Wani dalibi da ya sha da kyar daga harin ‘yan bindigan ya shaida wa Aminiya cewa, shi ma Allah (SWT) ne kawai ya tsirar da shi domin kuwa kadan ya rage harsashin ‘yan bindigan ya same shi, kodayake ya dan goge shi a hannunsa a yayin da yake gudu. A cewarsa wadannan maharan suna da yawan gaske don ta ko’ina harbi suka rika yi a cikin makarantar tasu , kuma ba zai iya cewa ko mutane nawa ba ne suka rasu ba, don shi a wannan dare ya gudu zuwa wani kauye da ke kusa da su ne, wato kauyen Baba Aura, a nan ya samu mafaka shi da wadansu abokansa da suka samu nasarar tserewa.
Dag a gari ya waye a wannan ranar mafi yawa daga cikin mazauna garin na Mamudo sai suka tere daga garin domin gudun kada su hadu fushi jami’an rundunar tsaron hadin gwiwa (JTF) alhali ba su ne suka yi wannan aika-aikar ba.
Kakakin rundunar tsaron JTF da ke kula da jihar Yobe Laftan Eli Lazarus ya tabbatar da faruwar wannan danyen aikin, amma ya ce a saninsa dalibai 20 ne suka rasa rayukansu da kuma wani malaminsu daya a sanadiyyar wannan hari na ‘yan bindiga. Sai dai kuma akwai 4 daga cikin daliban suna kwance rai kwakwai, mutu kwakwai da kuma wadansu da suka ji raunukasu na kwance a babban asibitin Potiskum suna karbar magani.
Sai dai kuma kakakin rundunar tsaron bai yi karin haske ba a kan ko jami’an rundunar sun samu nasarar cafke wadansu ba daga cikin maharani ba, amma kuma ya nemi jama’a da su rika ba su rahoton duk wadanda ba su gane da take-takensu ba da suka shigo cikinsu.
Haka kuma wani da ya ce shi jigo ne a kungiyar Jama’atu ahlussanh lid-dawa’atu wal-jihad, da aka fi sani da Boko Haram, Imam Muhammad Marwan a hirarsu da kafar watsa labaran sashen Hausa na Rediyo Faransa FRI cewa ya yi kungiyarsu ba ta hannu cikin kai wannan harin.
Shi kuwa da ya ke jawabi lokacin da ya ziyarci makarantar ta Mamudo don gane wa idonsa irin ta’asar da aka yi, Gwamna Ibrahim Gaidam na Jahar Yobe ya nuna rashin jin dadinsa ne dangane da faruwar wannan aika-aikar, ya yi fatan Allah (SWT) ya jikan daliban da suka hadu da irin wannan bala’in, Ya kuma bada hakurin jure wannan rashi ga iyayen daliban, su kuma wadanda ke kwance a asibiti gwamnan ya yi musu addu’ar samun sauki, inda ya kuma umarci hukumar asibitin garin na Potiskum da ta bada magani kyauta ga daliban.
Gwamnan ya kuma roki gwamnatin tarayya da hukumomin tsaron kasa da su yi wa Allah su dawo da hanyoyin sadarwar da al’umma ke amfani da su a jihar, kasancewar hakan zai bada damar samun rahoton maboyar ‘yan bindigar da sauran bata-garin da ke karekaina a cikin jihar da ma sauran jahohin makwabta don magance su cikin lokaci ba tare da sun yi barna ba.