Kisan Farfesa Ahmad Falaki
Marigayi Farfesa Ahmad Mustapha Falaki, kafin a kashe shi Darakta ne a Cibiyar Nazarin Aikin Gona (Institute of Agricultural Research (IAR)) da ke karkashin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. An kashe shi ne a kan hanyarsa ta dawowa daga wata ziyara da ya kai kauyen Yada-Gungume da ke karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi. […]
Marigayi Farfesa Ahmad Mustapha Falaki, kafin a kashe shi Darakta ne a Cibiyar Nazarin Aikin Gona (Institute of Agricultural Research (IAR)) da ke karkashin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. An kashe shi ne a kan hanyarsa ta dawowa daga wata ziyara da ya kai kauyen Yada-Gungume da ke karamar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi. Al’amarin ya faru ne a lokacin da Falaki ya umarci direbansa ya tsaya don su sauya tayar motarsu da ta samu matsala a lokacin da suke kan hanyarsu daga Jihar Bauchi zuwa Kano, a cikin motar har da kanensa. A lokacin da suke kokarin sauya tayar, wadansu mutane a kan Babura suka dira musu, sannan suka bukaci direban Falaki ya mika musu makullin motarsu, ganin yanayinsu ya sanya marigayin ya umarci direbansa ya mika masa makullin motar. Bayan sun kwace motar (kirar Hilud), sannan suka bar babur dinsu a wurin. Daga nan ’yan kauyen suka taru a wurin da al’amarin ya faru don yi wa su marigayin jaje.
Marigayi Falaki ya kira daya daga cikin matansa mai suna Rukayya, ya kuma sanar da ita abin da ya faru, sannan ya sanar da ita suna cikin koshin lafiya, suna kokarin ganin yadda za su dawo gida, don haka a fada wa ’yan uwa da abokan arziki su kwantar da hankalinsu.
Kwatsam sai ’yan sanda suka zo wurin, sannan suka fara gabatar da wadansu tambayoyi dangane da baburan da suka gani a wurinsu marigayi Falaki. Daga nan marigayin ya nuna musu katin shaidar aikinsa. Ba zato da tsammani ’yan sandan suka fara harbe-harbe, kafin a fahimci wani abu Farfesa ya mutu.
’Yan sanda a Jihar Kano sun fitar da wata sanarwa cewa wadansu ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kai wa ofishin ’yan sanda da ke karamar Hukumar Jibiya hari. Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, ASP Magaji Musa Majiya ne ya fitar da sanarwar, inda ya bayyana sun samu nasara fatattakar ’yan bindigar, sannan ’yan bangar garin sun hallaka daya daga cikin ’yan bindigar, sun kuma kama biyu daga cikinsu.
’Yan sanda a Jihar Kano sun ce wadansu makasa ne suka kashe Falaki, abin mamakin shi ne rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi ta fitar da sanarwa, inda ta bayyana cafke wadansu mutane biyu da ake zargin ’yan fashi ne, wadanda suka tabbatar da su ne suka kashe Falaki.
Wadannan sanarwa da ’yan sandan Jihar Bauchi da na Kano suka fitar sun bambanta da bayanin da Rukayya matar marigayi Falaki ta yi, inda ta ce mijinta ya ce barayi ne suka kwace musu motarsu. kanen marigayi mai suna Abba Mustapha da kuma direban marigayin sun yi bayanin da ya yi daidai da na Rukayya.
Abbas ya bayyana ya Falaki ya nuna wa ’yan sanda katin wurin aikinsa a lokacin da suka zo wurin da aka jefar da baburan, don wani dalili da su suka sani sai suka harbe shi.
Dangane da batun bayyana abin da ya faru za a iya cewa akwai lauje cikin nadi dangane da bayanan da ’yan sandan jihohi biyun suka fitar.
Matakin da iyalin marigayi Falaki suka dauka na rubuta wa Sufeto Janar na ’yan sanda wasika, tare da bayyana masa irin kisan gillar da aka yi wa Falaki da kuma zargin ’yan sanda da hannu dumu-dumu cikin al’amarin. Abin takaici ne a ce ’yan sanda sun ki bin yadda doka ta tanada dangane da al’amari irin wannan, wato duk wadda ake zargi ba mai laifi ba ne face kotu ta tabbatar da hakan.
Ko a al’amarin da yake nuna mutum mai laifi ne ’yan sanda ba su da damar daukar doka a hannunsu har su kashe mai laifin. Falaki ba ya dauke da makami, mene ne dalilin da za a kashe shi? Abin da ’yan sanda suka yi abin alla-wadai ne, babu wani uzuri da za su bayar.
Hukumar ’yan sanda ta ce ta sanya a yi bincike dangane da batun kashe Falaki, don haka ya zama dole a yi kwakkwaran bincike, sannan a hukunta duk wanda aka samu da laifi, don ya zama izna ga na baya don kada irin haka ta sake faruwa a gaba.