Kisan Farfesa Falaki: Iyalansa sun ce suna da ja kan rahoton ’yan sanda
Iyalan marigayi Farfesa Ahmad Mustapha Falaki sun bayyana rahoton da Ruundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta fitar cewa tana tuhumar wasu jami’anta shida kan kisan Farfesan a matsayin wani abu mai kama da “kare kai.” A ranar Larabar makon jiya ne Rudunar ’Yan sandan ta ce tana tuhumar wasu jami’anta shida kan nuna halin ko-in-kula […]
Iyalan marigayi Farfesa Ahmad Mustapha Falaki sun bayyana rahoton da Ruundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta fitar cewa tana tuhumar wasu jami’anta shida kan kisan Farfesan a matsayin wani abu mai kama da “kare kai.”
A ranar Larabar makon jiya ne Rudunar ’Yan sandan ta ce tana tuhumar wasu jami’anta shida kan nuna halin ko-in-kula da lamarin, inda a gabansu aka kashe Farfesan.
A cikin takardar da iyalan suka fitar dauke da sa hannun mai magana da yawunsu Aminu Daneji sun bayyana cewa babu gaskiya a cikin rahoton da ’yan sandan suka fitar inda suka dora laifin kisan ga mutanen kauyen Fala. “Taron manema labarai da ’yan sandan Kano suka yi kan kisan gillar da aka yi wa Farfesa Falaki a ranar 14 ga Fabrairu, daga rahoton da suka fitar mun gano cewa rundunar ta gaza gudanar da bincike na gaskiya, inda a karshe ta dora laifin kisan a kan mutanen kauyen Fala,” inji shi.
A cewar iyalan Farfesan “Game da labarin da shaidun gani da ido suka bayar sun bayyana cewa hadin gwiwar ’yan sanda a Rurum da Kibiya suka gudanar da kisan dan uwanmu Farfesa Falaki. Ko a lokacin da aka kwace motar su Farfesan ba a samu mutanen garin sama da mutum 12 da suke tare da Farfesan kafin ’yan sandan su zo wurin da kaddamar da mummunan aikinsu ba. A nan ba gaskiya ba ne a ce sama da mutum dubu biyu sun far wa Farfesan sun kashe shi,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Tun farko rahoton da ’yan sanda suka fara fitarwa shi ne sun kashe wani da ake zargi dan Boko Haram ne sannan sun kama biyu daga cikinsu.”
Ya ce wannan rahoton ba abin dogara ba ne, abu ne kawai na wanke kai, don haka idan ana so su gamsu da sakamakon a ba wasu mutane na daban masu zaman kansu ragamar gudanar da binciken, amma ba ’yan sandan ba.
Ya kara da cewa suna sanar da jama’a cewa tunda ta tabbata ’yan sanda sun gaza gudanar da bincike a kan lamarin, saboda haka iyalan marigayin sun shirya da lauyoyisnu domin daukar mataki a kai.
A makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan ta ce tana tuhumar wasu jami’anta shida wadanda take zargi da sakaci kan kashe Farfesa Falaki, kuma ta gabatar da wasu mutum biyu a gaban kotu kan kashe shi din.