Kisan Farfesa: kungiyoyin malamai da ma’aikatan jami’a na son a sake bincike

kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta nemi Rundunar ’Yan sanda da ta sake bincike kan batun kisan gillar da aka yi wa Farfesa Ahmad Mustapha Falaki da aka kashe shi mako biyu da suka gabata. Shugaban kungiyar ASUU ta kasa Dokta Nasir Fagge ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Kano, inda […]

Kisan Farfesa: kungiyoyin malamai da ma’aikatan jami’a na son a sake bincike
Kisan Farfesa: kungiyoyin malamai da ma’aikatan jami’a na son a sake bincike

kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta nemi Rundunar ’Yan sanda da ta sake bincike kan batun kisan gillar da aka yi wa Farfesa Ahmad Mustapha Falaki da aka kashe shi mako biyu da suka gabata.

Shugaban kungiyar ASUU ta kasa Dokta Nasir Fagge ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Kano, inda ya ce duk da cewa rundunar ta ce ba jami’anta ne suka kashe Farfesan ba, akwai bukatar a sake gudanar da bincike kan lamarin. “Muna kira ga Mataimakin Sufeton Yan sanda na kasa mai kula da Shiyya ta daya Tambari Yabo Mohammed ya sake gudanr da bincike don a gano wadanda suka gudanar da kisan tare da hukunta su daidai da laifinsu.
Ya ce akwai takaici game da hanyar da Farfesan ya rasu, duk da kokarin bayani ga ’yan sanda bayani ganin yana da yakinin zai samu tsira a wurinsu. “Akwai takaici kan yadda ’yan sanda suka ki yarda da katin shaidar Farfesan har a karshe ya rasa ransa a gabansu ba tare da sun hana hakan ba. Babu shakka Farfesa Falaki ya rasu da tunanin cewa zai samu kariya daga ’yan sandan. Amma maimaikon haka sai suka dauke shi da sauran abokan tafiyarsa a matsayin ’yan Boko Haram da suka kai musu hari a ofishinsu da ke garin Kibiya,” inji shi.
Su ma kungiyoyin ma’aikata da ba na koyarwa ba a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sun bukaci Gwammatin Tarayya ta bi diddigi domin zakulo wadanda suka yi wa Farfesa Falaki kisan gillar.
kungiyoyin da suka hada da ta manyan ma’aikata (SSANU) da ta ma’aikatan nazarin aikin gona (NAAT) da ta ma’aikatan da ba na koyarwa ba (NASU) sun fadi ta bakin Shugaban kungiyar SSANU Malam Iliyasu A. Bello a ranar Talata cewa sun ji takaicin yadda ’yan sanda suka jagoranci jama’ar gari wajen yi wa Farfesa Falaki kisan gilla da sunan Boko Haram duk da ya nuna masu takardar shaidar aiki. “Wannan na nuna cewa jami’an tsaron kasar na ba su mutunta takardar shaida ko ba su da ilimin fahimtar sakon da takardar shaidar ke isarwa. Wannan na nuna cewa dubban mutanen da ba su san hawa ko sauka ba na rasa rayukansu da sunan yaki da Boko Haram a hannunsu,” inji su. Sun bukaci gwamnati ta tabbatar an bayyana wa al’umma sakamakon binciken da za a gudanar, kuma a zakulo baragurbin ’yan sanda masu kisan jama’a da sunan Boko haram.