Kisan Filato: An binne mutanen da aka kashe a Jos

Mutane da dama a yankin sun nemi Gwamnatin jihar ta ɗauki mataki tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.

Kisan Filato: An binne mutanen da aka kashe a Jos

An binne mutanen da aka kashe a harin Anguwan Rukuba da ke Jos ta Arewa a Jihar Filato.

Adadin mutanen da suka rasu a harin da aka kaiya kai 33 kuma an binne su a ranar Talata a jihar.

’Yan bindiga sun kai hari a daren ranar Lahadi, inda suka riƙa harbe-harbe kan jama’a, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Da farko an ruwaito cewar mutum 28 ne suka rasu, amma daga baya wasu sun rasu a asibiti.

A wajen jana’izar da aka yi a cocin ECWA, wakilin gwamnati ya ce gwamnati na ƙoƙarin gano waɗanda suka kai harin tare da kawo ƙarshen rikicin.

Ya kuma tabbatar wa iyalan mamatan cewa za a yi musu adalci.

Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a Jihar Filato, ya ce ba za a samu zaman lafiya ba sai an yi adalci, inda ya yi kira ga  gwamnati ta ɗauki mataki.

An lokacin gudanar da jana’izar wasu mata da matasa sun yi zanga-zanga suna neman a saki wasu matasa uku da aka kama bisa zargin suna da hannu a harin.

Sun ce matasan ba su da laifi.

Zanga-zangar ta lafa bayan an samu labarin cewa an saki matasan uku, lamarin da ya daidaita al’amura a yankin.

Daga nan ne aka ci gaba da gudanar da jana’izar cikin lumana.

Wani mazaunin unguwar ya ce an kama matasan ne kwanaki kaɗan bayan kari harin.

A gefe guda kuma, wani mai sharhi kan al’amuran jama’a ya gargaɗi mutane da su guji yi wa binciken jami’an tsaro katsa-landan ta hanyar zanga-zanga.