Kisan gilla: An fara binciken sojoji kan kashe Fulani 11 a Kaduna
’Yan uwa da al’ummar garin tabbatar cewa gawarwakin na wasu Fulani 11 ne da sojoji suka kama a lokuta daban-daban
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta fara bincike kan kisan gilla da ake zargin dakarunta sun yi wa wasu Fulani 11 a yankin Ladduga da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.
Shugabannin Fulani a kauyen Tilde Fulbe da ke Ladduga sun shaida wa wakilinmu cewa wani babban jami’in dan sandan sojoji mai muƙamin Birgediya-Janar ya je kauyen domin gudanar da bincike.
A makon jiya ne wakilinmu ya ruwaito yadda aka tsinci wasu rubabbun gawarwakin Fulani 11 a dajin da ke kusa da yankin “Crossing” a karamar hukumar.
’Yan uwa da al’ummar garin tabbatar cewa gawarwakin na wasu Fulani 11 ne da sojoji suka kama a lokuta daban-daban a yankin.
- Yadda sababbin hare-hare ke firgita mazauna Abuja
- Yadda harin sojoji ya sauya rayuwar mutanen Tudun Biri a Kaduna
Wani shugaban Fulanin Ladduga, Ayuba Muhammad ya shaida wa wakilinmu cewa ranar Asabar sojoji sun je gudanar da bincike a yankin.
Ya ce, “Ina tabbatar da cewa wani dan sandan sojoji mai muƙamin Birgediya-Janar ya zo, inda ya yi mana wasu tambayoyi game da kisan gillan.
“Mun kuma tabbatar masa da cewa mu ne muka ba wa kafar yada labarai ta Daily Trust duk bayanan da ke cikin rahoton da suka wallafa.”
Ayuba ya kuma tabbatar cewa babu wanda sojojin suka yi wa wata barazana a yayin binciken suka gudanar.
Tun bayan bullar rahoton dai masu fafutikar kare hakkin dan Adam suke ta kira da a gudanar da bincike kan kisan gillar da ake zargin sojoji sun yi wa Fulani 11 a yankin na Karamar Hukumar Kachia.
Daga cikinsu, wani lauya, Barista Muhammad Nura, ya ce sojoji ba su da hurumin kashe mutum ba tare da umarnin kotu ba.
Don haka ya bukaci Rundunar Tsaro ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano masu hannu a ciki da kuma hukunta su.