Kisan gilla: Sakkwatawa sun ba Buhari wa’adin kwana 14 ya je musu ta’aziyya

Suna bukatar Buhari ya biya diyyar barnar da ’yan bindiga ke yi tunda gwamnati ta kasa magance matsalar.

Kisan gilla: Sakkwatawa sun ba Buhari wa’adin kwana 14 ya je musu ta’aziyya

Wata zanga-zanga a Jihar Sakkwato bayan kisan gilla da aka yi wa matafiya. (Tsohon hoto).

Daliban Jihar Sakkwato sun ba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wa’adin kwana 14 ya ziyarci jihar tare da biyan diyyar mutanen da ’yan bindiga suka yi wa kisan gilla ko barna.

Taron Kungiyar Shugabannin Daliban Jihar Sakkwato ta ce ziyarar Buhari zuwa jihar ta zama babu makawa, saboda yadda ’yan bindiga ke yawan yi wa mutanen jihar kisan gilla.

“Muna kira ga Shugaban Kasa ya yi duk shirin da zai yi ya ziyarci Jihar Sakkwato cikin kwana 14 ya gane wa kansa, ya kuma tattauna da kwamandojin yaki domin ya gano matsalatar da ke hana samun ci gaba a yaki da ’yan bindiga a jihar,” inji daliban.

Sakataren kungiyar, Muhammad Aminu, ya ce, idan kwana 14 ta cika ba tare da Buhari ya yi abin da suka bukata ba, to za su bullo masa ta wata hanyar.

Ya shaida wa maneman labarai cewa, “Yanzu haka ba mu da kwanciyar hankali a jiharmu, bisa dukkan alamu kuma gwamnati ta fita batun mutanen Jihar Sakkwato.

“A halin yanzu yankin Gabashin Jihar Sakkwato na ganin tashin hankali iri-iri, da ke lakume rayukan dubban mutane da lalata dukiyoyinsu da garuruwansu gami da garkuwa da mutane da korar manoma daga gonakinsu na gado

“Har yanzu Gwamantin Tarayya ta kasa magance wadannan ayyukan ta’addancin, duk kuwa da tabbacin da ta sha bayarwa.”

— A tura isassun jami’an tsaro da kayan aiki

Don haka suka bukaci gwamnati ta tura wadatattun jami’an tsaro da kayan aikin da suke bukata su fatattaki ’yan bindigar a duk inda suke ba tare da bata lokaci ba.
Sannan ta yi wani ingantaccen tsari na biyan diyya ga duk mutanen da ayyukan ’yan bindiga suka yi wa barna, domin su samu yadda za su ci gaba da rayuwarsu.

“Gwamnati ta sani cewa Jihar Sakkwato a Najeriya take, ta kuma yi duk abin da ya kamata na kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa kamar yadda doka ta tanada sannan ta tabbata babu wani yanki na kasar nan da ke hannun ’yan bindiga ko masu taimaka musu.

“Wajibi ne gwamnati ta tashi ta kare manoma da gonakinsu ganin yadda matsalar karancin abinci ke barazana ga ’yan Najeirya,” inji daliban.