Kisan gilla ya jefa daliban Mashood Abiola cikin ni‘ya-su

Tsoro da fargaba sun addabi daliban makarantar fasaha ta Mashood Abiola (MAPOLY) dake Abeokuta, Ogun.daliban sun sami kansu ne a wannan hali yayin da aka kashe mutane hudu lokacin da lokacin da wasu gaggan kungiyoyin asiri biyu ke karanbatta da junaa a makon da ya gabata. Kashe-kashen ya abkune a sassa daban daban na unguwar Oluwo da […]

Kisan gilla ya jefa daliban Mashood Abiola cikin ni‘ya-su
Kisan gilla ya jefa daliban Mashood Abiola cikin ni‘ya-su

Tsoro da fargaba sun addabi daliban makarantar fasaha ta Mashood Abiola (MAPOLY) dake Abeokuta, Ogun.
daliban sun sami kansu ne a wannan hali yayin da aka kashe mutane hudu lokacin da lokacin da wasu gaggan kungiyoyin asiri biyu ke karanbatta da junaa a makon da ya gabata.
Kashe-kashen ya abkune a sassa daban daban na unguwar Oluwo da Adigbe dake  karamar hukumar Obafemi Owode, unguwanin da mafi yawancin daliban makarantar ke zaune.
Ana kyautata zaton mutum hudu da aka kashe daliban makarartar ne. Hakan ya sanya da dama a cikinsu suka tsare daga dakunan kwanansu sakamakon samamen  da rundanar ‘yan sanda ke kaiwa wajan tun faruwar wannan al’amarin.
Kashe-kashen dai ya afku ne sakamakon gwabzawar da ‘yan  kungiyar asiri da ake  kira da Eiye ta yi da takwararta ta Buccaneer.
daya daga cikin daliban da aka kashe ranar Lahadi, mai suna Muraina Ibrahim wanda akewa lakabi da Elebe yana  karatun diploma ne a fannin  fasahar na’ura  maikwalkwaluwa. dalibi na biyu wanda aka kashe ranar Asabar din da ta gabata shima dalibine dake karatun difuloma a fannin sadarwa. Wannan kashe-kashen sun farune a unguwannin SAP da Macjob. An tabbatar da cewa duka daliban biyu ‘yan aji biyu ne a makarantar.
Babu cikakken bayanan ragowar daliban gabanin lokacin hada wanan labarin said dai an kashe daya ne a unguwar Mango a ranar asabar dayan kuma a Iyan oloke.
Jami’i mai Hulda da Jama’a Na makarantar, Mista Sulaiman Adebiyi ya tabbatar ya sami labarin kisan mutum hudun sai dai yace bashi da tabaccin ko daliban makarantar MAPOLY ne ko a’a. Ya kara dacewa ‘yan sanda sun kame dalibai 8 sakamakon kashe-kashen.
Amma wasu daga cikin dalibai sunce kamen da ‘yansanda suka yi kame na na maiuwa da wabi. daya daga cikin shugabannin dalibai yace ‘yan sandan  sun fara kai sumame ne a ranar Asabar a inda suka kame dalibai da dama a unguwanni k Bar a Adigbe yayinda a ka kame wasunsu a tashoshin dake daura da makarantar.
Jami’in hulda  da jama’a na  rundunar ‘yan  sandan  Jahar Ogun  Muyiwa Adejobi, ya bada  tabbacin kame dalibai 9 wadanda ake alakantawa da kashekashen kana yace sun dade suna samun korafe-korafen ta’asar kungiyoyin asirin a unguwannin da daliban ke zaune a inda yaja hankulan dalibai da su kare martabarsu su guji  shiga kungiyoyin asiri.