Kisan gillar Zamfara: Gwamnati da jama’a na nuna wa juna yatsa

A yayin da aka kasa samun cikakken adadin mutanen da aka kashe a kisan gillar Zamfara, ana cigaba da samun zargin gwamnatin jihar da hannu a cikin irin abin da ke faruwa da mazauna kauyukan da ake kashe mutane.Sanata Sa’idu dansadau ya zargi gwamnati da hannu a cikin hari, yayin da Kwamishinan Labarai Ibrahim Muhammad […]

Kisan gillar Zamfara: Gwamnati da jama’a na nuna wa juna yatsa
Kisan gillar Zamfara: Gwamnati da jama’a na nuna wa juna yatsa

A yayin da aka kasa samun cikakken adadin mutanen da aka kashe a kisan gillar Zamfara, ana cigaba da samun zargin gwamnatin jihar da hannu a cikin irin abin da ke faruwa da mazauna kauyukan da ake kashe mutane.
Sanata Sa’idu dansadau ya zargi gwamnati da hannu a cikin hari, yayin da Kwamishinan Labarai Ibrahim Muhammad Birnin Magaji da Mai ba Gwamnan Shawara, Sani Abdullahi Tsafe da takwaransa Alhaji Magaji Dosara, suka shiga gidan rediyo suka dirar wa Sanata dansadau, suna cewa gwamnatin Abdul’aziz Yari ba ta da hannu a cikin kashe-kashen, kuma tana kashe makudan kudi don shawo kan lamarin.
Wakilanmu da suka ziyarci ’Yar Galadima, inda ake zargin an kashe sama da mutum 150, wani da bai sao a ambaci sunansa ya ce: “Wallahi Malam kafin faruwar wannan hari, watanmu bakwai ba mu barci a gidajenmu sai a waje ko a gefen gari. Yanzu haka babu mai saniyar noma guda daya, kuma wani abin mamaki shi ne yadda za a ce kusan duk wanda aka harba za ka samu a kai aka same shi. Kuma babu barawon da ba a san gidansa ba.”
Alhaji Garba danmaliki daya daga cikin wadanda suka yi hidimar gawarwakin ya ce abin da ya ba su mamaki shi ne yadda kashi tamanin na wadanda aka harba a kai aka same su.
Malam Adamu Madu, Magajin ’Yar Galadima cikin bacin rai cewa ya yi: “Wa za mu mulka idan aka kashe mana mutane? Shugabanninmu sun gaya wa gwamnati ba sau daya ba, ba sau biyu ba amma babu magani, yanzu watanmu bakwai babu mai kwana gidansa, sharar gona kawai in ka je za a kashe ka, baburan da gwamnati ta ba Fulani da ake kira Boko Haram da manyan motoci da su aka zo aka kashe jama’a.”
Ya ce suna cikin karbar gaisuwar sai da aka kwashe masu shanu sama da 40 kuma da faruwar harin an kora musu shanu sama da 250. Ya ce idan dan banga ya kashe Bafulatanin da ake zargi da satar, sai a kama shi a kulle, amma idan Bafulatani barawon shanu ya kashe wani ya kashe banza ba abin da za a yi.
Mai unguwar ya ce abin da ya sa suke zargin gwamnati shi ne an kashe wa, an kashe kane, an kashe uba, sun kai kara amma a banza. “An kashe mutane a dangulbi da
Kabaro da Kizara ga shi yanzu a ’Yar Galadima kuma babu wanda aka kama.
Yanzu haka ana zargin barayin sun taru a wasu dazuzzuka da ke yankin, kamar dajin Galeji a dangulbi da Gobirawan Chali da ’Yar Galadima da na Hannun Kangon Fari.