Kisan Gombe: Majalisa ta umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki

Majalisar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta kafa rugagen zamani a jihohi 36 don inganta tsaro da haɓaka rayuwar makiyaya da manoma.

Kisan Gombe: Majalisa ta umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki

Majalisar Dattawa ta buƙaci Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Shugaban Hafsan Sojoji, da Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta DSS, su binciki kisan gillar da ’yan bindiga suka yi wa mutane a Ƙaramar Hukumar Billiri a Jihar Gombe.

Majalisar ta kuma buƙaci hukumomin tsaro su kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Har ila yau, ’yan majalisar sun roƙi Gwamnatin Tarayya da ta kafa rugagen zamani a jihohi 36 na Tarayya da Babban Birnin Tarayya, don inganta tsaro da haɓaka rayuwar makiyaya da manoma.

Majalisar ta kuma shirya gabatar da dokar da za ta fayyace iyakokin harkokin tattalin arziƙi da aka amince da su ƙarƙashin yarjejeniyar ECOWAS kan ‘yancin zirga-zirga tsakanin ƙasashe.

Waɗannan ƙudurorin sun biyo bayan gabatar da ƙudiri daga Sanata Anthony Siyako Yaro (Gombe ta Kudu), wanda ya nuna buƙatar magance hare-haren ‘yan bindiga.

Ya koka kan kashe-kashe da korar mutane da mahara ke yi daga gidajensu a wasu ƙauyukan da ke Ƙaramar Hukumar Billiri.

Sanata Yaro, ya tunatar da majalisar cewa gwamnatin na da haƙƙin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ƙara da cewa, “Mai girma shugaba, dole ne mu ɗauki mataki kan abin da ‘yan bindiga ke aikatawa, musamman a yankin Arewa.”

Bayan tattaunawa, Majalisar Dattawa ta buƙaci a kafa rundunar haɗin gwiwa ta ’yan sanda da sojoji a Ƙaramar Hukumar Billiri domin daƙile ayyukan mahara.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja