Kisan Goni Aisami: Kotu Za Ta Bayyana Ranar Yanke Hukunci Na Karshe 

Babbar Kotun Jihar Yobe na shirin yanke hukunci ga wasu sojoji biyu da aka gurfanar kan kashe Marigayi Sheikh Goni Aisami

Kisan Goni Aisami: Kotu Za Ta Bayyana Ranar Yanke Hukunci Na Karshe 

Sheikh Goni Aisami

Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zamanta na shirin yanke hukunci kan wasu sojoji biyu da aka gurfanar kan kashe Marigayi Sheikh Goni Aisami bayan kammala sauraren shari’ar kisan kai.

A watan Augustan shekarar 2022 aka kama sojojin kan halaka malamin ta hanyar bindige shi a hanyar Kano zuwa Gashua, inda aka kama su a cikin motarsa.

Wannan shari’ar da ke tsakanin Gwamnatin Jihar Yobe da wadannan mutane biyu, Kofur John Gabriel da Adamu Gideon, ta tattara shaidu da dama da aka gabatar.

A ranar Laraba mai shigar da kara ga gwamnatin jihar, Barista  A.S Mohammed, da kuma Barista D.M mai kare wadanda ake kara, suka yi muhawararsu ta karshe.

Kofur John Gabriel ya amsa a gaban Alkalin kotun cewa, shi ne ya kashe fitaccen malamin addinin Musuluncin kamar yadda ake zargin sa da aikata.

Bayan alkalin kotun, Mai shari’a Usman Zanna Mohammed, ya saurari dukkan hujjoji da bayanan da bangarorin suka gabatar, ya dage zaman domin yanke hukunci na karshe wanda nan gaba za a sanar.

Dangane da wannan shari’a ta kisan gillar da aka yi wa Sheikh Goni Aisami, a kullum ’yan uwa da abokan arziki hade da al’ummar Musulmai ke jiran ganin irin hukuncin da za a yanke wa mutanen.

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Lamari Game Da Harin Sojoji Kan Al’umma A Sakkwato