Kisan Hanifa: An ci gaba da shari’ar Abdulmalik Tanko

Yanzu haka an ci gaba da shari’ar Abdulmalik Tanko wanda ake tuhuma da kashe marigayiya Hanifa

Kisan Hanifa: An ci gaba da shari’ar Abdulmalik Tanko

Abdulmalik Tanko da Hanifa, yarinyar da ake tuhumarsa da kashewa a Kano

An sake gurfanar da malamin makarantar nan da ake zargi da yi wa dalibarsa mai shekara biyar, Hanifa Abubakar, kisan gilla.

Yanzu haka an ci gaba da shari’ar Abdulmalik Tanko wanda ake tuhuma da kashe marigayiya Hanifa bayan ya yi garkuwa da ita.

An gurfanar da Abdulmalik Tanko a kotu ne bayan dubunsa ta cika, inda ya amsa cewa ya kashe Hanifa, wadda daliba ce a makarantarsa.

Tuni dama kotu ta sa aka tisa keyarsa zuwa gidan yari, a yayin da ta ba da umarnin tsare matarsa, wadda ake zargi da hada baki da shi a hannun ’yan sanda.