Kisan Hanifah: Abdulmalik ya ƙalubalanci hukuncin kisan da aka yanke masa

Abdulmalik Tanko, malamin da ya kashe ɗalibarsa Hanifah Abubakar a Kano ya ɗaukaka ƙara yana neman a soke hukuncin kisa da kotu ta yanke masa.

Kisan Hanifah: Abdulmalik ya ƙalubalanci hukuncin kisan da aka yanke masa

Abdulmalik Tanko da Hanifa, yarinyar da ake tuhumarsa da kashewa a Kano

Abdulmalik Tanko, malamin makarantar nan da kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin kashe ɗalibarsa Hanifah Abubakar ’yar shekara biyu a Kano ya ƙalubalanci hukuncin.

Abdulmalik ya ɗaukaka kara ne yana neman kotu ta soke hukuncin da aka yanke masa.

A ranar 28 ga watan Yulin 2022 ne Mai Shari’a Usman Mallam Abba na Babbar Kotun Jihar Kano ya yanke wa Abdulmalik da abokinsa Hamisu Isyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da laifin yin  garkuwa da Hanifah da kuma kashe ta.

Marigayiya Hanifah dai ita ce kaɗai iyayenta suka haifa kafin ta gamu da ajalinta a hannun Abdulmalik.

Idan ba a manta ba, a baya Abdulmalik ya amsa laifin kisan ɗalibarsa Hanifah Abubakar mai shekaru biyu.

A baya Aminiya ta ruwaito shi yana bayyana cewa ya sace ta ne sannan ya yi amfani da shi kafar ɓera wajen hallaka ta ya binne ta a yankin Ƙaramar Hukumar Nassarawa da ke Jihar Kano.

Sun kitsa akwai gaba da Hanifah ne a hanyarta ta komawa gida daga makaranta, inda suka kai ta makarantar makarantarsa, ya kashe ta.

Bayan watanni da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, lauyansu, Barista Anthony Ezenwoko, ya ɗaukaka ƙara tare neman a janye hukuncin.

Abdulmalik Tanko yana neman a soke hukuncin da aka yanke masa ne bisa hujjar cewa kotun farko ta yanke hukuncin a bisa kuskure.