Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Za mu shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu zafin kishin Musulunci.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
- Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
- Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu zafin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
Aminiya ta ruwaito yadda Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa Najeriya tana nan daram a matsayin ƙasar da ba ta lamunci cin zarafi saboda addini ba, yana mai nanata dimokuraɗiyyar Najeriya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.
A martanin da ya yi wa Trump, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tun lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2023, tana ci gaba da gudanar da tattaunawa da duka shugabannin Kiristoci da Musulmai domin ƙarfafa haɗin kai da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga kowane yanki da addini.
“Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga addinai daban-daban da yankuna.”