Kisan Manoma: Sojoji da mafarauta sun ɓace bayan harin ISWAP

Sun gano gawarwaki manoma 60, amma 15 daga ciki suka iya binnewa a sakamakon harin kwanton ɓauna da mayaƙan ISWAP suka kai musu

Kisan Manoma: Sojoji da mafarauta sun ɓace bayan harin ISWAP

Sojoji da jami’an Sibiliyan JTF da mafarauta da suka tafi ɗauko gawarwakin manoman nan sama da 40 da Boko Haram ta yi wa kisan gilla a yankin Kukawa da ke Jihar Borno sun ɓace bayan mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kai musu harin kwanton ɓauna.

Majiyoyi sun cewa tawagar sojojin da ’yan Sibiliyan JTF da matasa kimanin 60 da suka je ɗauko gawarwakin sun ɓace tun bayan harin da mayaƙan suka kai musu a hanyarsu ta zuwa Dumba Baga, inda Boko Haram t yi wa manoman kisan gilla.

Wata majiyar Sibiliyan JTF ta ce sojojin sun mayar da martani, amma mayaƙan na ISWAP suka ci ƙarfinsu a yayin artabun na ranar Talata.

Majiyar ta mutum daya ne kacal ya dawo Kukawa daga cikin ’yan Sibiliyan JTF da matsa 54 da ke cikin tawagar da ta tafi aikin ɗauko gawarwakin.

“Ba za a iya cewa ga haƙiƙanin halin da ake ciki ba saboda babu cikakken bayani; mutum ɗayan da ya dawo ba a cikin hayyacinsa yake ba da za a yi magana shi,” in ji majiyar.

Amma wata majiyar tsaro ta ce wasu daga cikin sojojin da aka tura sun koma sansanisu bayan musayar wutar da suka yi da ’yan ta’addan, bayan sun gano tare da binne gawarwakin wasu daga cikin manoman.

Ta ce, “Sun gano gawarwakin manoma 15 sun binne su, amma daga bisani ’yan ta’addan suka kai musu ƙazamin hari a yayin da suke shirin ƙarasawa zuwa Dumba.

“A hanyar Dumba suka ga gwarwakin manoman a yashe, suka binne 15, amma daga baya aka kawo musu hari kafin su ci gaba da tafiya.

“Sojoji da fararen hula da dama da ke tawagar farko sun ɓace tun ranar Talata, ba mu sani ba ko ’yan ta’addan ne suka yi garkuwa da su ko kuma suna daji,” in ji majiyar tsaron.

Wani jami’in Sibiliyan JTF ya ce,  “Abin da tashin hankali, ba zan iya faɗin yawan waɗanda suka ɓace ba, amma muna roƙon Allah Ya dawo mana da su lafiya.

“Fararen hula kimanin 70 ne ke cikin tawagar, amma ’yan kaɗan ne kawai suka dawo, sun gano gawarwaki manoma 60, amma 15 daga ciki suka iya binnewa a sakamakon harin kwanton ɓauna da aka kai musu,” in ji shi.