Kisan miji: Kotu ta ba da belin Maryam Sanda

Wata Babbar Kotu a Abuja, da take yin shari’ar Maryam Sanda da ’yan sanda suke tuhuma da kashe mijinta Bilyaminu Bello ta bayar da belinta a shekaranjiya Laraba. A baya, alkalin kotun Mai shari’a Yusuf Halilu ya ki amincewa da belin nata har karo hudu da lauyanta ya nema, sai a karo na biyar ya […]

Kisan miji: Kotu ta ba da belin Maryam Sanda

Wata Babbar Kotu a Abuja, da take yin shari’ar Maryam Sanda da ’yan sanda suke tuhuma da kashe mijinta Bilyaminu Bello ta bayar da belinta a shekaranjiya Laraba.

A baya, alkalin kotun Mai shari’a Yusuf Halilu ya ki amincewa da belin nata har karo hudu da lauyanta ya nema, sai a karo na biyar ya amince da batun belin, bayan da lauyanta, Joseph Daudu (SAN) ya bijiro da hujjojin cewa tana fama da rashin lafiya kuma tana dauke da ciki dan wata uku.

Mai shigar da kara, CSP James Idachaba ya ki amincewa da batun belin, amma Mai Shari’a Yusuf Halilu ya amince da hujjojin da lauyan Maryam ya kawo, inda bayan ya gabatar da takardun rahoton likita da ke tabbatar da yanayin ciwon da ke damunta, sai kuma ya bayyana cewa tana bukatar kulawa ta musamman kuma ba za ta iya samun haka ba a gidan jarun, saboda ba su da ingantattun kayan kula da lafiyar majinyata masu laulayi irin nata.

A yayin bayar da belin, Mai Shari’a Yusuf ya bukaci Maryam ta gabatar wa kotu mutum biyu da za su tsaya mata belin, wadanda suka mallaki gidaje a Abuja, sannan kuma mahaifinta ya rubuta takardar alkawarin cewa zai rika kawo ta kotu a duk lokacin da shari’a ta bukace ta.

Mai Shari’a Yusuf Halilu  ya dage shari’ar zuwa ranar 19 ga Maris domin ci gaba da sauraren karar.