Kisan mutane 37 a Tureta: Gwamnatin Sakkwato ta ba da tallafin N45m

Gwamnatin jihar ta bayar da tallafin Naira miliyan 30 da buhunan shinkafa 300 ga iyalan waɗanda aka kashe.

Kisan mutane 37 a Tureta: Gwamnatin Sakkwato ta ba da tallafin N45m

Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Idris Muhammad Gobir, ya yi kira ga al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.

Gobir ya yi wannan kiran ne lokacin da ya kai ziyarar jajantawa ga waɗanda suka tsere daga ƙauyen Ɗangulbi da ke Ƙaramar Hukumar Tureta bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai, inda suka kashe mutum 37 a hare-hare biyu cikin kwanaki uku a makon da ya gabata.

Ya ce jami’an tsaro kaɗai ba za su iya kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga ba tare da haɗin kai da goyon bayan al’umma ba.

“Babban nauyin da ya rataya a wuyan kowace gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa. Saboda haka, gwamnatin Ahmad Aliyu na ci gaba da ɗaukar matakai domin kawar da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a faɗin jihar,” in ji shi.

Mataimakin gwamnan ya jajanta wa al’ummar yankin tare da addu’ar Allah Ya gafarta wa mamatan.

Daga nan ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 30 da buhunan shinkafa 300 ga iyalan waɗanda aka kashe.

Haka kuma, gwamnatin jihar ta ba da tallafin buhunan shinkafa 1,200 da Naira miliyan 10 ga ’yan gudun hijirar da ke yankin, sannan ta ware Naira miliyan biyar domin kula da waɗanda suka jikkata sakamakon harin.

Gobir ya kuma roƙi kwamitin da aka kafa domin raba tallafin da ya tabbatar da an yi adalci wajen rabon kayan da kuɗaɗen tallafin.

Tun da farko, muƙaddashin Shugaban Ƙaramar Hukumar Tureta, Alhaji Umar, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa kulawar da ta nuna tare da tallafin da ta kai wa waɗanda lamarin ya shafa.

Shi ma Wakilin Uban Ƙasar Tureta, Malam Bashir Sani, ya bayyana farin cikinsa tare da gode wa gwamnatin jihar kan ziyarar jaje da tallafin da ta kawo wa al’ummar yankin.