Kisan mutum 51a Kaduna: ‘Yadda muka tsira daga ’yan bindiga’
Mazauna kauyuka hudu da ’yan bindiga suka kai wa hari a Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna sun ce ba su taba ganin bala’i irin wanda suka gani a ranar Lahadin da ta gabata ba. Mahara sun shiga kauyukan Kerawa da Marina da Gwada da Zareyawa, inda suka kashe akalla mutum 51, sannan suka […]
Mazauna kauyuka hudu da ’yan bindiga suka kai wa hari a Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna sun ce ba su taba ganin bala’i irin wanda suka gani a ranar Lahadin da ta gabata ba.
Mahara sun shiga kauyukan Kerawa da Marina da Gwada da Zareyawa, inda suka kashe akalla mutum 51, sannan suka kone gidaje da motoci da kayan abinci da babura.
’Yan Boko Haram ne suka kawo mana hari – inji wani
Daya daga cikin ’ya sintirin daya daga cikin kauyukan da abin ya shafa ya bayyana wa Aminiya cewa: “Mun dawo daga sintirin da muke yi da misalin karfe 5:30 na Asuba sai muka nufi masallaci domin yin Sallah kafin mu koma gidajenmu mu rama barci. Kafin a kammala Sallah sai muka ji karar babura na shigowa cikin garinmu wanda abu ne da ba mu saba ji ba. Da muka leka sai muka fara jin karar harbe-harbe saboda dama mun san hakan na iya faruwa wadansunmu na da jiko wadansu kuma ba su da shi. Wadanda ke da jiko ana harbinsu amma harsashi ba ya shiga. Wanda bindiga ba ta ci shi ba sai su bi shi da babur su buge shi su kuma caccaka masa abu a kai har sai sun kashe shi.”
Ya ce, “Sun kona mana motoci shida sun kashe mutum 13 a kauyen Marina inda suka fara kai hari, akwai makwabtanmu mutanen garin Kerawa da suka kawo mana dauki amma sai aka yi musu kwanton bauna a kan hanya. A Kerawa an kashe mutum 23 sun kona motoci da babura sun kuma tafi da wasu babura.”
Game da ko akwai sa-in-sa a tsakaninsu da ’yan bindigar sai ya ce “Babu wata sa-in-sa a tsakaninmu da su, domin mu dai muna kare garinmu ne don gudun kada a fado mana kuma ba wani wuri muke zuwa ba, iyakacinmu yankinmu. Idan suna da sa-in-sa da jami’an tsaro wannan tsakaninsu ne. Kuma gwammati na samar da jami’an tsaro ne don kare jama’a su kuma abin da ba su so ke nan. Kuma tunda jami’an tsaro sun fi karfinsu shi ne suka fado mana.”
A kan ko an kawo musu harin ne saboda mutanen kauyukan na bai wa jami’an tsaro bayanai a kan ’yan ta’addan kamar yadda ake zargi, sai ya ce, “Lailai akwai batun masu sanar da su haka. Domin ai ko Annabi ya zauna da manafukai. An samu irin haka a garin Gwada da sauransu an samu matsaloli da ke nuna idan mugu ya shiga hannu bayan ya fito akan samu manafukai da za su fada masa ai da wane da wane ne suka sa aka kama shi. Daga nan shi kuma sai ya nemi yadda zai hallaka mutum ko kuma tilas ya sa mutum barin garin.”
“Mu dai a shirye muke mu kare garuruwanmu idan za mu samu goyon bayan jami’an tsaro. Kuma za mu bayyana mugun da ke cikinmu ko waje, Don haka muna kira ga gwamnati ta taimaka mana da jami’an tsaro a wannan yanki namu,” inji shi.
Wani mutumin kauyen Kerawa ya shaida wa Aminiya cewa, “Gaskiya ba ma zargin maharan masu garkuwa da mutane ne, a ganinmu ’yan Boko Haram ne domin a babura suke kusan 200. Sun kuma kwashe sa’o’i uku zuwa hudu suna barna ba tare da wani jami’in tsaro ya zo ba.”
Wani mutumin kauyen Marina ya ce akalla kauyuka 13 aka tayar a cikin ’yan watannin nan a yankin Kerawa. Ya ce ba su taba ganin bala’i irin wanda suka gani ba a wannan rana da mutanen suka kewaye garin.
Ya nanata cewa a ganinsu maharan ’yan Boko Haram ne ba barayi ba, domin babu abin da suka dauka na hatsi sai kashe mutane kurum da suka yi.
Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige ya ce a iya fahimtarsu harin da aka kai wa mutanen ba ya da alaka da bayanai ko goyon baya da jama’ar yankin ke bai wa jami’an tsaro.
Ya ce ko harin da jami’an tsaro suka kai wa ’yan ta’addan a yankin Birnin Gwari har aka yi nasara karkashen su a kwanaki ba ta yankin Kerawa suka bi ba.
“Mun ziyarci yankin da abin ya faru na kuma gana da dattawan yankin a kan abin da ya faru kuma babu wanda ya kawo wannan magana da kake yi yanzu,” inji shi.
Don haka sai ya ce tuni an tura jami’an tsaro har da sojoji zuwa yankin kuma suna ci gaba da neman maharan, don haka sai ya nemi jama’a su daure su ci gaba da ba su bayanai da za su taimaka wajen gano maboyar mutanen a kan lokaci.
‘Yadda muka tsira daga maharan’
Wakilinmu ya ziyarci wasu daga cikin kauyukun da lamarin ya shafa tare da ziyartar wadansu da suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga a asibitocin da suke jinya.
A Asibitin Kauran Wali inda aka kai mutum bakwai da aka raunata, mutum hudu sun rasu a sakamakon raunin harbin, saura mutum biyu.
Daya daga cikinsu, mai suna Bilyaminu ya ce, “Ina zaune a Kerawa da ke Karamar Hukumar Igabi. A safiyar Lahadin suka auka wa Unguwar Marina da ke kusa da mu da harbe-harbe kuma muka ga wuta na ci a garin don haka sai muka tattara jama’armu don mu kai musu dauki. Muna shirin shiga garin sai kawai muka ga sun kewaye mu, duk inda ka duba sai su kawai kake gani, sai suka yiwo kanmu da harbin kan mai uwa da wabi, sai duk muka tarwatse duk wanda suka samu sai harbe shi. A haka ne suka harbe ni a ciki, inda daga baya aka kawo ni nan.”
Mutum na biyu da ke kwance a asibitin mai suna Muhammad, Ya ce, “Ina zaune a kauyen Marina ne da ke Kerawa a Karamar Hukumar Igabi, da na ji karar harbin bindiga, ko da na waiga sai ga su a kusa, sai na ruga a guje da kafa suna bi na da babura har sai da suka same ni sannan suka harbe ni a ciki, sai suka wuce suka bar ni a kwance. To shi ne bayan abin ya dan yi sauki sai aka kawo ni nan, kuma an yi min aiki a cikin.”
Wakilinmu ya kuma ziyarci Asibitin Iyatawa Nursing Conbalacent Home da ke kan hanyar Birnin Gwari, inda mutane 8 ke kwance suna jinya, wani dattijo mai suna Sa’idu Yusuf ya ce, “Maharan sun shigo kauyenmu na Kerawa suna ta harbin mutane da suka zu gidanmu suka kashe min dan uwa mai suna Idi, domin sun harbe shi amma bindigar ba ta kama shi ba, sai suka rika caccaka masa bakin bindiar har sai da kansa ya fashe kwanyarsa ta fito waje, sannan sai suka sa wa gidan wuta. Ni kuma da kwanana bai kare ba sai raunin harbin bindiga na samu a hannu.”
Shi ma Adamu Rabi’u cewa ya yi, “Ina masallaci bayan idar da Sallar Asuba sai muka ji karar bindiga. Da na fito daga masallaci sai ga su nan, wadansunsu a babura wadansu da kafa, babu inda zan gudu don haka sai na tsaya kawai. Ina tsaye sai suka harbe ni a kafada sai na fadi sannan suka wuce, amma sun kashe min iyayena da wani daga cikin kannena.”
Wani datijo kuma shugaban al’umma da aka sakaya sunansa ya ce, “A ranar farko mun samu gawarwaki 19 na mutanen Kerawa sai 13 na mutanen Marina kuma dama su ne wadanda aka fara kai wa harin, sai Zareyawa mutum 7 sai kuma na garin Ma’ajimawa mutum 3. A ranar an samu gawar mutum 43.
“Sojoji sama sun kai wa ’yan ta’addan hari ta sama kuma da alama sun raunata su sosai. ’Yan gudun hijira sun fara komowa gidajensu, kuma kamar yadda ka gani ’yan uwa da abokan arziki na ta kawo mana ziyarar tausayawa kuma ko jiya Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i ya zo ya yi alkawarin daukar mataki.”
Wani matashi da ke zaune a garin Galadawa a Karamar Hukumar Giwa mai suna Rabilu da ya tsalake rijiya da baya bayan da wadansu da ake zargin suna cikin ’yan bindigar suka kai masa hari a daren Litinin, suka sassare shi da makamai, an ce sun yi masa haka ne saboda ya nuna jin dadinsa kan yadda gwamnati ta dauki mataki a kan ’yan ta’addan. Matashin wanda yanzu ke jinya, an ce ya fito fili a kauyensu yana murna lokacin da jami’an tsaro suka kai hari dajin Birnin Gwari a kwanakin baya inda aka ce sun kashe ’yan bindiga da dama. Kuma ana jin hakan ne ya sa ’yan ta’addan kai masa hari a gida ranar Litinin din.
Wani mai bada gudunmawa ya ce sun dade ba su yin barci da dare saboda matsala tsaro. Ya ce, “Akwai garuruwan da ’yan ta’addan suka samu shinge kuma kowa ya sani tsawon lokaci in kai ba nasu ba ne ba dama ka shiga wadancan wurare kuma kusan duk kowane gida akwai wakilinsu wanda dama su ne ke ba mu wahala.
“Akwai garin Garke da Madugu da Baushe da Tornoku da Sabon Gida da Unguwar Idi da Hayin Gazari. Wadannan wurare kusan babu gidan da ba su da wakili a ’yan ta’addan , kuma ka ga abin da ya faru da daya daga cikin yaranmu. Wai kawai a kan ya yi murnar sojojin na kai wa ’yan ta’adda hari, shi ma suka kai masa hari wai hakan ya zama darasi ga duk mai murna. Sun dauka sun kashe shi ne,” inji shi.
Wani da ya nemi a boye sunansa ya ce sun fara hangen nasara sakamakon yadda gwamnati ta dauki lamarin saboda kusan yawancin ’yan ta’adda suna da masu kai musu rahoto.
Ya ce jami’an tsaro sun yi karancin da ba za su iya tunkarar ’yan ta’adda ba saboda yadda suke kwarara zuwa ta’addancin, amma idan aka gyara hanyar sadarwa ta yadda za a iya tantance duk wani bayani na sadarwa za a samu sauki. Sai ya nemi jama’a su rika yawaita addu’a.

Ku yi mana hakurin gazawa wajen kare ku – Gwamna El-Rufa’i
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya ziyarci wadanda aka kai wa harin, inda ya nemi afuwarsu kan harin da aka kai musu. “Na zo ne domin in ba ku hakuri domin gaza kare ku. Muna yin iyakacin kokarinmu domin rage faruwar irin wannan lamari. Muna kokarinmu, don haka muna sa ran za mu shawo kan lamarin domin akwai jami’an tsaro a kasa da suke ta kokari a kan lamarin,” inji shi.
Ya ce “Mun umarci jami’an tsaro su tarwatsa ’yan bindigar nan, har sai mun mayar da su zuwa ga Ubangijinsu, kuma jami’an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba. Jami’an tsaro za su bi su har cikin daji domin murkushe su.”
Gwamnan ya ce jami’an tsaro sun kawo dauki a harin ta sama da ta kasa, “Jami’an tsaron suna samun tsaiko ne saboda wasu hanyoyin zuwa kauyukan ba su da kyau, sannan mutanen kauyukan suna samun matsala wajen isar da sakonnin abubuwan da ke faruwa cikin sauri saboda matsalar rashin ingantaccen layin waya. Amma muna godiya ga sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro,” inji shi. Sai ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu.
Gwamna El-Rufa’i ya kuma bukaci Hukumar SEMA ta kai wa wadanda abin ya shafa kayan agaji don tallafa musu.