Kisan Nafiu: Kotu ta sa a sake auna kwakwalwar Hafsat Chuchu
Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin sake gwada lafiyar kwakwalwar Hafsat Suraj (Chuchu) a asibitin gwamnatin jihar, sannan ci gaba da tsare ta a gidan yari na Kurmawa. Kotun da ke zamanta a titin Miller ta bayar da umarnin ne a ci gaban shari’ar zargin Hafsat Chuchu kan kisan wani “yaron gidanta” mai […]
Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin sake gwada lafiyar kwakwalwar Hafsat Suraj (Chuchu) a asibitin gwamnatin jihar, sannan ci gaba da tsare ta a gidan yari na Kurmawa.
Kotun da ke zamanta a titin Miller ta bayar da umarnin ne a ci gaban shari’ar zargin Hafsat Chuchu kan kisan wani “yaron gidanta” mai suna Nafiu Hafiz.
Tunda farko kotun ta karbi sakamakon gwajin kwakwalwar da aka kawo daga Asibitin Kula da Kwakwalwa na Gwamnatin Tarayya da ke Dawanau.
Aamma Mai sharia Zuwaira Yusuf ta bayar da umarnin a sake gwada lafiyar kwakwalwar wacce ake tuhuma a Asibitin Kula da Kwakwalwa na Gwamnatin Jihar.
- Boko Haram ta kona gidajen da aka gina wa ’yan gudun hijira a Borno
- Alkawura 5 da Abba ya yi wa Daurawa da ’yan Hisbah
A cewar Mai Shari’a Zuwaira, ‘Daga baya zan auna tare da tantance tsakanin sakamakon biyu don kotu ta yi adalci.’
Aminiya ta rawaito cewa a zaman kotun da ya gabata, Mai Shari’a Zuwaira ta bayar da umarnin auna kwakwalwar Hafsat Chuchu a asibiti.
A wani ci gaban kuma kotun ta hana belin mijin Hafsat (Dayyabu Abdullahi) da Adamu Muhammad da Nasidi Muhammad da aka gurfanar kan zargin bayar da bayanan karya da nufin kange Hafsat daga fuskantar hukuncin kisan da ta yi wa Nafiu.
Alkalin kotun Mai sharia Zuwaira Yusuf ta bayyana cewa laifin da ake tuhumarsu da shi laifi ne babba wanda ba zai yiwuba bayar da belin Kai tsaye ba sai dai tare da wasu hujjoji.
“Ba a bayar da irin wadannan hujjojin a takardar neman belin ba don haka na hana belinsu”
Sai dai ta bayar da umarnin fara sauraren shaidun akan abin da ya shafi shariarsu.
Lauyoyin wadanda ake tuhuma Barista Sani Ammani da Haruna Magashi da Rabiu Abdullahi sun nemi kotun ta sa lokacin sauraren shaidu a kusa kada ya wuce kwanaki 14 ko kuma a rika sauraren shaidun a kullum dogaro da sashe na 390(3)(4) na Kundin Shariar Laifuffuka na Jihar Kano.
Daga karshe alkali ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga Maris, 2024 don ci gaba da sauraren shari’ar.