Kisan Sarkin Gobir: ‘Za mu maka Gwamnatin Sakkwato a Kotun Duniya’

Suna zargin Gwamnatin da sakaci, saboda ita ce ta gayyaci Sarkin Gobir zuwa Sakkwato, amma ta gaza ba shi kariya ko kuɓutar da shi

Kisan Sarkin Gobir: ‘Za mu maka Gwamnatin Sakkwato a Kotun Duniya’

Gamayyar kungiyoyin matasa kungiyar sun yi barazanar maka Gwamnatin Jihar Sakkwato a Kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) kan yin sanadin kisan gillan da ’yan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir Alhaji Isa Muhammad Bawa bayan sun yi garkuwa da shi.

Gamayyar kungiyoyin matasan karkashin inwuar Ƙungiyar Matasan Afirka ta Neman Sasanci da Zaman Lafiya, ta zargi Gwamnatin Sakkwato da sakacin da ya haddasa kisan gillar da aka yi wa Sarkin Gobir.

Shugaban ƙungiyoyin matasan guda 18, Dokta Suleman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana haka ne bayan wani taron kwana biyu da suka kammala.

Ya ɗora laifin kisan da ka yi wa Sarkin Gobir kan abin da ya kira halin ko-in-kula da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta nuna.

Don haka ya ba ta wa’adin mako biyu ta biya musu buƙatunsu ko kuma su maka ta a gaban kotun ICC.

Ya ce, buƙatun su ne: “A sallami kwamishinan tsaron jihar, a biya diyya ga iyalan  Sarkin Gobir sannan gwamnatin jihar ta fito ta bayyana matsayinta kan kisan sarkin.

“Muna zargin Gwamnatin da yin sakaci ne saboda ita ce ta gayyaci Sarkin Gobir din zuwa Sakkwato domin halartar taro, amma ta gaza ba shi kariya.

“Uwa uba kuma, ta kasa kuɓutar da shi bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da shi.”

Kokarin wakilinmu na yin magana da Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Sakkwato, Bello Sambo Danchadi da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Abubakar Bawa, bai yi nasara ba.

Dukkansu babu wanda ya ɗaga waya ko amsa rubutaccen sakon da aka tura masa.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano