Kisan sojoji a Neja: ’Yan ta’adda sun debo ruwan dafa kansu
Hafsan soji guda na hannun ’yan bindiga da suka kashe sojoji shida, ciki har da hafsoshi biyu a Jihar Neja.
Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da rasuwar dakarunta shida ’yan bindiga suka kashe a Jihar Neja.
Daraktan yada labaran rundunar, Edward Buba, ne ya bayyana wa wakilinmu cewa “Waɗanda suka yi wannan mummunan aiki za su ɗanɗana kuɗarsu, za su samu mummunan sakamako.”
A daren Juma’a ce ’yan bindiga suka yi wa sojojin kwanton bauna suka kashe su akauyukan Roro da Kagara da Rumace a gundumar Bassa da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Baya hafsoshi biyu da kananan sojoji hudu da ‘yan ta’addan suka kashe, sun kuma yi garkuwa da wani mai mukamin Kyaftin.
- Tinubu Ya Karrama Sojojin Da Aka Kashe A Delta
- NAJERIYA A YAU: Ana Zargin Juna Tsakanin APC Da NNPP Kan Sake Dakatar Da Ganduje
Wannan lamari ya faru kusan wata guda bayan wasu mahara a garin Okuama da ke Karamar Hukumar Ughelli ta Kudu ta Jihar Delta sun kashe sojoji 17 da ke kan hanyarsu ta zuwa aikin wanzar da zaman lafiya kan wani rikicin filaye a yankin.
Yayin zantawarsa da wakilinmu, Manjo Janar Buba, ya ce, “Abin takaici ne mun sake rasa wasu dakarunmu da ke aikin tsaron kasa da ’yan kasa.
“Ina tabbatar maka, akwai sakamako mai muni da zai biyo bayan wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
“Za mu farauto su kuma mu gurfanar da su kan abin da suka aikata.”
Kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu, ya bayyana kisan sojoin a matsayin koma baya na wucin gadi.
Amma ya ce wasu sojojin sun kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda bayan faruwar lamarin, kuma sun yi nasarar kashe da dama daga cikinsu.
“Sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’addar da suka yi musu kwanton bauna, inda suka kashe ‘yan ta’addan da dama suka kama wasu da ma kayan aikinsu,” in ji shi.