Kisan Sojoji: Basaraken da ake nema ya miƙa kansa ga ’yan sanda
Rundunar sojin Najeriya ta ayyana sunayen mutum takwas da ta ke nema ruwa a jallo kan kisan dakarunta.
Basaraken Ewu an-Urhobo, Mai martaba Clement Oguenerhukewe Ikolo, ya mika kansa ga rundunar ’yan sandan Jihar Delta, bayan ayyana sunansa a matsayin wanda ake nema kan kisa dakarun sojin Najeriya.
Basaraken dai na daya daga cikin mutum takwas da rundunar Najeriya ta ayyana a matsayin wadanda ta ke nema ruwa a jallo.
- CBN ya yi wa bankuna ƙarin jarin da za su mallaka
- Addu’a ya kamata Malamai su riƙa yi wa Najeriya ba la’anta ba — Tinubu
Basaraken ya mika kansa ga ’yan sandan ne sa’o’i kadan bayan sojoji sun bayyana sunansa a matsayin daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a kisan sojoji 17 a kauyen Okuam da ke Jihar Delta.
Kafin mika kansa ga ‘yan sanda, basaraken ya gana da ’yan jarida, inda ya bayyana mamakin yadda sunansa ya fito a cikin wadanda ake nema.
“Na yi matukar mamakin yadda sunana ya bayyana a cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo.
“Ba ni da hannu a kisan da aka yi, ba ni da hannu wurin hada baki da wani ya kashe kowa, ya saba wa falsafar da nake da ita, a matsayin ɗan Adam, da kuma aƙidata a matsayina na ɗan ɗariƙar Katolika”.
Ya kara da cewa “Wannan abin da aka yi babban laifi ne, abin da ya kamata su yi shi ne su duba wuraren da abin ya faru, su gudanar da cikakken bincike domin a tabbatar da adalci.
“Ni ba ni da bangare, gwamnatin jihar tana sane da tashe-tashen hankulan da nake fama da su, kuma ta san shirin da nake yi na gayyatar ɓangarorin da ke rigima da juna, kafin wannan mummunan abu ya faru.”
Sarkin, ya bayyana cewa a halin da ake ciki ba shi da majalisa a matsayinsa na basarake saboda rashin jituwar da ke tsakanin jama’arsa.
Ya kara da cewar bai san komai dangane da kisan da aka aikata ba.
Amma ya bayyana kaɗuwarsa kan yadda sunansa ya fito a matsayin wanda ke da hannu a mummunan kisan dakarun sojin.
Idan ba a manta ba a farkon watan Maris ne, wasu bata-gari suka yi wasu dakarun soji 17 da ke aiki da bataliya ta 18 a jihar kisan gilla.
Sojojin dai na kokarin aikin sulhu ne a tsakanin wasu kabilu da rikici ya barke musu.