Kisan sojoji: Buhari ya yi ganawar gaggawa da hafsoshin tsaro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ganawar gaggawa da shugabannin tsaro tare da Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya akan kisan da mayakan Boko Haram suka yi wa sojojin Najeriya. An dai gudanar da ganawar sirrin ne a fadar shugaban kasa Abuja jiya Lahadi. Harin da aka kaiwa sojojin a kauyen Metele da ke jihar […]

Kisan sojoji: Buhari ya yi ganawar gaggawa da hafsoshin tsaro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ganawar gaggawa da shugabannin tsaro tare da Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya akan kisan da mayakan Boko Haram suka yi wa sojojin Najeriya.

An dai gudanar da ganawar sirrin ne a fadar shugaban kasa Abuja jiya Lahadi.

Harin da aka kaiwa sojojin a kauyen Metele da ke jihar Borno ya yi sanadiyar rasuwar sojoji da dama.

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da: Shugaban jami’an tsaro, Janar Gabriel Olonisakin, shugaban rundunar sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, shugaban sojojin sama, Iya Mashal Abubakar Sadiq, shugaban sojojin ruwa, Bayis Adimiral Ibok-Ete Ibas, Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris da kuma Darakta Janar na Hukumar tsaron DSS, Yusuf Magaji Bichi.