Kisan ta’addanci ya karu da ninki uku a duniya
Wani bincike da aka gudanar kan ayyukan ta’addanci a duniya ya bayyana cewa adadin mutanen da ’yan ta’adda suka kashe ya karu da kashi 61 cikin 100, wato ya ninka kusan sau uku a bara.Binciken, wanda Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki da Zaman Lafiya ta Duniya (IEP) ta wallafa, ya ce kusan mutum dubu 18 ne […]
Wani bincike da aka gudanar kan ayyukan ta’addanci a duniya ya bayyana cewa adadin mutanen da ’yan ta’adda suka kashe ya karu da kashi 61 cikin 100, wato ya ninka kusan sau uku a bara.
Binciken, wanda Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki da Zaman Lafiya ta Duniya (IEP) ta wallafa, ya ce kusan mutum dubu 18 ne suka mutu a hare-hare dubu10 da aka kai a sassan duniya.
Binciken ya dora alhakin kashi biyu cikin uku na kashe-kashen a kan kungiyoyi hudu da suka hada da: kungiyar IS da ke Iraki da Syriya da Boko Haram a Najeriya da Al-ka’ida da Taliban a Afghanistan da Pakistan.
Rahoton ya bayyana cewa kasar Iraki ce ta farko a duniya wajen aikata ayyukan ta’addanci a duniya inda a shekara ta 2013 aka kashe mutum dubu 6 da 362 a hare-hare dubu 2 da 492 da aka kai. Sai kasar Afghanistan, wadda aka mata hare-hare sau dubu daya da 148 kuma aka hallaka mutum dubu 3 da 111.
Sauran sun ne Pakistan, wadda aka kai mata hare-hare sau dubu daya da 933, kuma mutum dubu biyu da 345 suka mutu. Sai Najeriya, wadda aka kai mata hare-hare sau 303 kuma mutum dubu daya da 826 suka mutu. Sai kuma Syriya da aka kai mata hare-hare sau 217 kuma aka hallaka mutum dubu daya da 78.
Shugaban Cibiyar IEP, Mista Stebe Killelea, ya shaida wa gidan rediyon BBC cewa an samu karuwar kashe mutane a hare-haren ta’addanci ne, sakamakon yakin basasar da kasar Syriya ta tsunduma a ciki a shekarar 2011.
Kuma binciken ya nuna cewa ayyukan ta’addanci na faruwa ne sakamakon tunzurawar da gwamnatoci ke yi wa ’yan ta’adda da kuma laifin da suke ganin ana yi musu ba domin dalili na talauci ba.