Kisan Ummita: Karar zabe ta kawo tsaiko ga shari’ar dan China

Shari’ar zabe ta sa an dakatar da sauraron shari’ar zargin dan kasar Chinan da kashe budurwarsa Ummulkulsum Sani Buhari (Ummita) a Kano

Kisan Ummita: Karar zabe ta kawo tsaiko ga shari’ar dan China

Dan China da Ummita

Sauraron kararrakin zabe ya kawo tsaikok ga shari’ar zargin dan kasar China da kashe budurwarsa Ummulkulsum Sani Buhari, wadda aka fi sani da Ummita a Kano.

A ranar 6 ga watan Afrilu ne ya kamaa kou a ci gaba da sauraron shari’ar Mista Frank Geng Quanrong wanda ake zargi da kisan Ummita, amma zaman kotunan sauraron kararrakin zaben 2023 da ke gudana a Najeriya ya sa aka dakatar.

Aminiya ta gano cewa an dakatar da ci gaban shari’ar kisan Ummita ne saboda alkalin, Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji, na daga cikin alkalan kotun sauraron kararrakin zabe a wajen jihar.

Kisan Ummita mai shekaru 23 da yanayin alakarta da Mista Quangrong dai ya jima yana tayar da kura.

Mista Quangrong dai ya amsa laifin kashe Ummita ta hanyar amfani da wuka, bayan da farko ya musanta zargin a gaban  Mai Shari’ar Sunusi Ado Ma’ai na Babbar Kotun Jihar Kano.

A yayin sauraren shari’ar dai, dan Chinan wanda ma’aikaci ne a wata masaka a Kano ya yi ikirarin kashewa wa masoyiyarsa Ummita sama da Naira miliyan 60, kafin daga bisani ya yi ajalinta a kan wata takaddama da suka yi da shi a gidan iyayenta.

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra