Kisan ya isa haka

Magana ta gaskiya yawan kashen jama’a da ake yi a kasar nan musamman a yankinmu na Arewa masifar ta ta’azzara. Yau da a ce wata kasa ce ta far wa kasarmu Najeriya a yankin Arewacinta, to, ko shakka babu a iya cewa wannan kasar ta yi nasara a kanmu. Domin irin yadda ake zubar da […]

Kisan ya isa haka
Kisan ya isa haka

Magana ta gaskiya yawan kashen jama’a da ake yi a kasar nan musamman a yankinmu na Arewa masifar ta ta’azzara. Yau da a ce wata kasa ce ta far wa kasarmu Najeriya a yankin Arewacinta, to, ko shakka babu a iya cewa wannan kasar ta yi nasara a kanmu. Domin irin yadda ake zubar da jini kullum, ta kowace kusurwa da bangare na Arewa abin ya yi yawa.’Yan Boko Haram su kashe, masu garkuwa da mutane su kashe, ’yan fafutikar kabilanci ko bangaranci su afka wa juna, masu da’awar bambancin addini su far wa junansu, aikin ke nan dai zubar da jini, ba dare ba rana.

Duk da kasancewar fitinar na ci wa kowa tuwo a kwarya, amma kusan kowa ya kasa yin wani katabus na a-zo-a-gani don magance ta, kowa gani yake kamar hukuma ce kawai ke da alhaki ko hanyoyin magance lamarin.

Sam abin ba haka yake ba. Ni a nawa tunanin, ina ganin idan har ba a tashi tsaye, tsayin daka ba, sauran al’ummomin kasar nan muka yi ba, ba abin da hukuma za ta iya yi, don haka duk da matakan da hukuma ke hawa, ba inda kwazonta ke kaiwa, domin ai hannu daya baya daukar jinka. Shi ya sa muke ganin dole sai an hada karfi da karfe, an goga gemu da gemu kafin a shawo kan lamarin nan. Wato abin nufin shi ne, sai an samu hadin kai da taimakon sarakuna da malaman addini da ’yan siyasa da masu hannu da shuni da talakawa da daukacin al’ummar kasa .

Sarakunan gargajiya: Abin da ya sa muke ganin sai da taimakon sarakuna shi ne, kowa ya san sarakuna su ne iyayen al’umma, su ne suka fi kusanci ga jama’a, kuma a yankunansu ne ake fara rura wutar fitinar da take zamowa tamkar wutar daji. Don haka idan dai akwai wani da ya kamata ya dakile wani tashin hankali ga al’umma,to, a bayansu yake.

Domin su ne suke fara ganin zuwan fitinar, su ne suke iya auna karfin fitinar, kaifinta da kuma gane gudunta. Kuma a mafi yawan lokuta, masu tayar da ita daga cikin jama’arsu suke bullowa. Idan da sarakunanmu suna mai da hankalisu cikin yin adalci da sasanci da sassauci da gaskiya da rikon amana a cikin zamantakewarsu ga talakawansu da kuwa sun samu karfin dakile wutar rikici cikin sauki da gaggawa a yankunansu, maimakon zaman jiran zuwan hukuma ta kawo musu daukin jami’an tsaro.

Malama addini: Malaman addini haske ne, domin su ne ke rike da fitilar (littafin) ilimin sanin Ubangiji da zamantakewa da makomar al’umma. To, me ya sa tashe-tashen hankula da zubar da jini suka yawaita a yankunanmu duk da yawan malaman addinin da muke da su? Abin da ya sa na yi wannan tambaya shi ne, wallahi duk inda ka ga mai kokarin ta da zaune-tsaye,ko shakka babu akwai jahilci  a tare da shi, domin dukan addinanmu sulhu da sasanci ne akida da koyarwarsu.

Amma kaiconmu al’ummar kasar nan, mafi yawan malaman sun daina haska zamantakewar talaka da wani ilimin da zai inganta rayuwarsa da shi balle ya sama masa zaman lafiya, sun koma haska wa fadar sarakuna da gidajen attajirai da na ’yan siyasa hanyoyin zaluntar talakawansu a hikimance, don kwadayin samun abin da za su shiga gasar saka manyan kaya na kasaita da motocin alfarma da gina gidajen hutawa a tsakaninsu. Sai kuma son girma da shahara da zukatansu suka jarabtu da su.

Amma da malaman addinanmu sun mai da hankalinsu wurin ilimantar da al’ummarsu son zaman lafiya da son juna da inganta rayuwarsu kamar yadda addinanmu suka zo da su  da yanzu ba mu san wata masifar tashin hankali da zub da jini ba. Kuma da malaman addinanmu sun mai da hankalinsu ga son sanin wane hali shugabanninmu ke mulkarmu da yaya alkalanmu ke hukunta mu da yaya zamantakewarmu da juna ke gudana don su wa’azantar da mu da mun zauna lafiya da junanmu.

’Yan siyasa: Ko shakka babu ’yan siyasa sun siyasantar da rayukanmu, domin a da, ba mu san da wadannan kashe-kashe da zubar da jini ba, sai da zuwan gurbatacciyar siyasa. Mu dai da zuciya daya muka karbi jadawalin siyasa a kasar nan, a lokacin da aka tallata mana manhajarta a 1999. Amma sai ga ta yanzu ta zame mana aibu da aikin da-na-sani. Da-na-sani mana, tunda da a ce a yau sojoji za su sake karbar mulki don mu samu zaman lafiya, wallahi da mun fi son haka,kuma da mun amince maimakon  wannan yanayi da wadansu batagarin ’yan siyasa suka saka rayukammu a ciki.

Ai dai ba a boye lamarin yake ba, na  yadda ’yan siyasa suka mai da wadansu matasanmu ’yan bangar siyasa, suka ba su makamai, suka ba su kayan maye, suka gurbata  tunaninsu, suka kekasar da zukatansu, kawai don cimma biyan bukatunsu na siyasa. To, yau ga shi irin aibin da hakan ya janyo mana. Don haka, ’yan siyasa ku sani wannan masifar da ta kunno kai ta kisan kiyashi da ake yi wa juna, ku ma ba za ta bar ku ba, domin ai abin da ya ci Doma ba zai bar Awai ba. Don haka ku canja taku da salo ko ma ceci yankimu da kasarmu da kawunanmu baki daya.

Masu hannu da shuni: Masu arziki kadai sun isa su samar da tsaro da zaman lafiya a kasar nan. Ta yaya? Ta hanyoyin rage radadin talauci da zaman kashe wando a tsakaninmu. Domin an yi ittifaki cewa duk inda ka ga rikici ya yawaita,to, ko shakka babu akwai talauci da rashin aikin yi a karkashinsa. Ba wai sai hanshakan masu arziki ne kadai mawadata ba, a’a, mawadata suna nan a tsakaninmu, domin duk wanda ya samu rufin asiri, to, ya  zama mai arziki.  Amma a yau masu kudin cikinmu sun kankame dukiyarsu,sun boye arziinsu, sun ma kasa sarrafa ta a cikinmu, ta yadda za a samu ayyukan yi da sana’o’i, su dai fatarsu da burinsu; wadatuwa sai dai su da iyalansu kadai. Da za ka duba kusa da kai, ka ga wa ke da bukata ka taimaka masa,ni ma in duba kusa da ni in taimaka, kuma ku duba,su ma su duba,wallahi da an samu wadatar da za ta samar da zaman lafiya a kasar nan. Ko kuwa muna zaton hukuma ce kadai  ke da alhakin wadata mu da tallafa mana mu azurta? A’a, wannan tsammanin namu kuskure ne. Mu dauki akidar tallafa wa ’yan uwanmu da makusantanmu mu gani, za ta wanzar da zaman lafiya mai dorewa a tsakaninmu, domin za ta sa mu so junanmu, mu bar kiyayya, sai ka ga an zauna lafiya.

Talakawa:

Talakan kasar nan musamman na yankin Arewa yana da hakurin danniya, keta da zaluncin da shugabanninsa ke yi masa. Shi ya sa da wuya ka ji talakawan kasar nan sun yi wa wani basarakensu ko shugabansu ko wani jagoransu bore ko tawaye, kuma duk da suna sane da ha’inci da zaluncin da ake yi musu ne silar talaucin da suke ciki. Amma kuma wani abin mamaki ga talakan kasar nan, sam ba ya kyamar talaucin nan da aka kakaba masa. A maimakon a samu yana kokari da fafutikar neman maganinsa ko hanyoyin rabuwa da shi, sai dai ka tarar da shi yana kokarin sarrafa shi (talaucin) da canja masa fasali salo-salo, ta yadda zai kara shakuwa da shi har ya dauwama a cikinsa. Haka ne mana, domin a yanzu da ake cikin yanayi na tashin hankali da zub da jini, wane ne ya rura wutar rikicin? Talaka. Wa aka cinna mawa? Talaka. Wa rikicin ya yi wa aibu da ta’adi? Talaka.

Domin ai shi ne ya rasa matsuguninsa, gonakinsa, kasuwancinsa, sana’o’insa da duk wani ci gabansa da na zuriyarsa. Koda yake ana ganin lallai akwai sa hannu wasu al’umomi irin su ’yan siyasa, bangaranci, kabilanci, addini da wasu kasashe na waje da suka zo mana da cunen wutar rikicin, amma kuma ai ba a gan su a zahiri (bayyane) ba, “Da dan gari akan  ci gari” inji Bahaushe, kuma hakan aka yi. Da a yau talakan Arewa ya kasance mai jin takaicin talaucin da yake ciki, mai fafutikar ficewa daga cikinsa, mai kishin zuci, mai kishin yankinsa da kasarsa, ai da wani bai yaudare shi ya ba shi bakin wuta ya cinna wa yankinsa ba. Bakin wuta mana, tunda ai manyan makamai ne ake rataya masa ya nufo ’yan uwansa don ya kashe su a matsayin maganin talauci. Wannan wane irin duhun jahilci ne,wace irin batacciyarr dabara ce; a biya ka ka kashe dangi da ’yan uwanka, ka hallaka muhallinka? To kai talaka idan ka gama hallaka yankinka, to, a ina zaka zauna ka ci arzikin  da kuma su wane ne za ka rayu ka ciki arzikin? Don haka muke gani dole shi ma talaka sai ya hankalta kafin a zauna lafiya.

Lallai ba shakka mu da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunanmu, sai har idan sarakunanmu da shugabanninmu sun yi mana adalci, malaman addinanmu sun rage son abin duniya, sun koma haska mana fitilar zaman lafiya, ’yan siyasa sun daina saka siyasa a zaman lafiyarmu, masu arziki sun rage hadama, talakawa mun san kishin kai da kishin kasarmu kafin mu san ‘Kisan ya isa haka’ har mu samu zaman lafiya. Ya Allah Ka zaunar da mu lafiya amin.

A’isha Usman Liman: 09093467171