Kisan ’Yan Arewa 3: Babu wani shiri na farautar ’yan Arewa a Enugu – Babban Limami

Babban Limamin Babban Masallacin birnin Enugu da ke kan titin Owerri, Alhaji Zulkarnaini Sa’eed ya ce kisan gilla da wasu mutane da ba a san ko suwa nene ba, suka yi wa wasu matasa uku ’yan Arewa a unguwar Ugwuaji da ke jihar, ba shi zai tabbatar da cewa makasan suna farautar ’yan Arewa ba […]

Kisan ’Yan Arewa 3: Babu wani shiri na farautar ’yan Arewa a Enugu – Babban Limami
Kisan ’Yan Arewa 3: Babu wani shiri na farautar ’yan Arewa a Enugu – Babban Limami

Babban Limamin Babban Masallacin birnin Enugu da ke kan titin Owerri, Alhaji Zulkarnaini Sa’eed ya ce kisan gilla da wasu mutane da ba a san ko suwa nene ba, suka yi wa wasu matasa uku ’yan Arewa a unguwar Ugwuaji da ke jihar, ba shi zai tabbatar da cewa makasan suna farautar ’yan Arewa ba ne da ke zaune a Jihar Enugu.
Limamin ya shawarci Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi da ya hanzarta daukar mataki wajen inganta harkokin tsaro, tun kafin munanan al’amuran su kara ta’azzara. Ya ce yadda wasu boyayyun mutane ke yi wa wadanda ba su ji ba kuma ba su gani ba kisan gilla yana bata sunan jihar.
Ya kuma shawarci masu sana’ar tuka motar Keke-Napep a jihar, musamman ma ’yan Arewa da su daina gudanar da sana’ar tasu da dare, domin kiyaye lafiyarsu, duk kuwa da cewa ana fuskantar matsin tattalin arziki a kasar nan.
Aminiya ta binciko yadda aka gano gawarwakin matasa uku, wadanda aka tabbatar da sunayensu da Babangida Sule da Ashahabu Dauda da Isma’ila Abdullahi, wadanda dukkansu masu sana’ar tuka Keke-Napep ne a Enugu. Kamar yadda ’yan sanda suka samu rahoto, an binne gawarwakin matasan ne a karkashin wata katanga da ake kan aikin ginawa a unguwar Ugwuaji da ke karamar Hukumar Enugu ta Kudu, inda kuma ’yan sandan suka ba da umurnin hako su a ranar Talatar da ta gabata, kuma aka same su har sun fara rubewa.
Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sanda a jihar, DSP Ebere Amaraizu ya bayyana wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, jami’an hukumarsu suna kan kokari dare da rana domin binciko hakikanin yadda al’amarin ya faru, tare da alkawarin bankado wadanda suka aikata ta’asar. Sai dai bai bayyana wa wakilin namu cewa ko ya zuwa yanzu sun kama wani ko ba su kama ba, dangane da kisan gillar. “Muna kan aikin binciken al’amarin kuma ina da yakinin cewa jami’anmu za su bankado tushen mafarin al’amarin.” Inji shi.
Kamar yadda Aminiya ta kalato, su dai wadannan matasa ’yan asalin yankin Arewa, an ce yi masu gani na karshe ne a ranar wata Asabar, 23 ga Janairun da ya gabata. Wasu daga cikin ’yan Arewa mazauna Enugun ne suka bayyana cewa a wannan rana ce suka yi masu gani na karshe a titin Owerri, cikin birnin na Enugu.
A wata tattaunawa da wakilinmu ya yi da wasu daga al’ummar Arewa mazauna Enugu, sun ce sun ga marigayi Sama’ila da misalin karfe 6:30 na maraice a unguwar Garriki, inda ya tsaya ya dauki fasinjoji a motarsa. Sun yi zargin cewa akwai yiwuwar mutanen nan da ya dauka, su ne suka halaka shi.
Shi kuwa Isma’ila Babangida, sun ce an gan shi ne da misalin karfe 10 na dare, yayin da yake shan shayi a sabuwar kasuwar Garriki, inda bayan ya kammala ya tafi aiki da motarsa, inda shi ma ake zaton fasinjan da ya dauka ne suka halaka shi, domin kuwa tun daga nan ba su kara ganinsa ba. A yayin da kuma suka ce shi Ashahabu, an gan shi ne a Babban Masallacin Enugu da ke kan titin Owerri, inda ya sallaci Magariba a jam’i, inda bayan ya kammala ya tafi neman fasinja da misalin karfe bakwai na dare.
daya daga cikin jami’an Babban Masallacin Enugu na kan titin Owerri, Umar Sulaiman, wanda kuma yana cikin wadanda suka fita neman matasan, ya bayyana wa Aminiya cewa, a lokacin da ba su ga matasan uku sun dawo ba a ranar Lahadi 24 ga Janairun da ya gabata, hankalin al’umma ’yan Arewa sai ya tashi, inda suka tafi ofisoshin ’yan sanda daban-daban suka kai rahoton cewa ba su ga ’yan uwansu ba.
A ranar Litinin 26 ga Janairun dai, sai muka ci gaba da cigiya ko’ina cikin birni. Muna kan nemansu ne, muna kan tafiya a unguwar Ugwuaji sai muka ci karo da ragar Keke-Napep din da Ashahabu Dauda ke amfani da ita.” Inji Umar.
Ya ci gaba da cewa, a lokacin da suka ci gaba da bincike, sai wasu yaran Ibo da ke kai-komo a wurin suka shaida masu cewa kada su shiga wani wuri da ke yankin. Tun daga lokacin ne suka fara zargin cewa to akwai wani abu, don haka nan take suka garzaya wajen ’yan sanda, suka kai rahoton al’amarin.
“Lokacin da muka jagoranci ’yan sanda zuwa wajen, sai muka samu wani wari na tashi, kuma muka ga wata tarin kasa. Muna kwashe kasar sai muka ga jar riga, wacce ta daya daga cikin matasan da muke nema ce. A yayin da muka ci gaba da hake kasar, sai kudaje suka rika baibaye wurin, inda bayan mun gama hakewa, sai muka samo gawarwakin matasan uku har sun fara rubewa.” Inji Umar.
Malamin ya ci gaba da cewa, bayan sun samo gawarwakinsu sai suka binne su a makabarta, daga bisani kuma suka je hedikwatar ’yan sanda domin rubuta jawabansu. “A lokacin da muke rubuta jawaban namu ne sai muka ga ’yan sanda sun shigo da daya daga cikin matasan Ibon nan da suka gargade mu cewa mu daina binciken wurin nan da muka gano gawarwakin.” Inji shi.
A yayin da yake karin bayani gane da al’amarin, Liman Sa’eed ya ce wannan al’amari ya bakanta ran ’yan Arewa mazauna Enugu da ma su kansu al’ummar Ibo ’yan asalin jihar. “Dukkanmu, Musulmi da Kirista ba mu ji dadin al’amarin nan ba, amma dai mu gane cewa wannan aika-aika ba ta tsaya kan ’yan Arewa kadai ba, domin kuwa a wurin da muka gano gawarwakin matasan nan, mun ga kasusuwan mutane da dama, wanda haka ke nuna cewa an dade ana kashe mutane a wurin nan.” Inji shi.
Ya ce duk da cewa gwamnatin jihar tana kokari ta bangaren tsaro amma ya kamata ta maida hankali wajen kula da jami’an tsaron kansu, domin kamar yadda ya ce, alama ta nuna cewa jami’an ba su maida hankali sosai wajen gudanar da ayyukansu yadda ya dace. “Inda muka gano gawarwakin matasan nan, ba ya da nisa da tungar ’yan sanda, inda suke bincike, amma ba su san da cewa ana kashe mutane a wurin ba har sai da ’yan uwanmu da kansu suka binciko wannan al’amari. Don haka ya kamata gwamnati ta yi wasu canje-canje ta fuskar tsaro a jihar, musamman akwai bukatar a kara yawan jami’an tsaron, domin ganin an kare al’umma a Jihar Enugu.”
Malam Sanusi Idris, wanda ya ce shi wa ne ga marigayi Isma’ila Babangida, ya ce a ranar Asabar da misalin karfe 2 na rana ya yi wa kanen nasa ganin karshe, kafin daga bisani ya ji labarin wai ya bace. Ya ce kanen nasa mutum ne mai fahimta da iya mu’amala da jama’a. Ya ce shi da kanen nasa su ’yan asalin karamar hukumar Toro ne da ke Jihar Bauchi. Ya ce marigayin ya mutu ya bar matarsa daya, wacce ba su kai ga samun haihuwa ba.
Ya bayyana cewa Babangida ya yi haya da Keke-Napep guda biyu wadanda ba nasa ba, amma sai ya yi kokari ya tara kudi har ya kai ga mallakar nasa na kansa. Mako biyu ke nan da mallakar nasa Keken sai aka halaka shi. “Sun kwace masa Kekje-Napep din kuma suka kashe shi. Ya kuduri aniyar gina rayuwarsa sosai, domin abin da ya so shi ne ya ci gaba da karatu, domin kuwa yakan dauki darasi da maraice, a wani tsarin kashin kansa da ya shirya da mai koya masa. Shekararsa 10 a Enugu yana gudanar da wannan sana’a ta tuka Keke-Napep.” Inji dan uwan nasa.
Haka kuma, Mataimakin Limamin Babban Masallacin Enugu, Alhaji Muhammadu Saminu Abdullahi ya ce shi kuwa marigayi Ashahabu Dauda, dan shekara 30 ne kuma ya zo Enugu ne daga Jihar Kano. Ya ce matashin yana da aure har ma da ’ya’ya uku. Ya ce ya zo Enugu ne tun tsawon shekaru bakwai da suka gabata.
Wakilin Al’ummar Arewa Mazauna Enugu, Alhaji Abubakar Yusuf Sambo, ya nemi gwamnati da ta tsaurara tsaro. Ya ce idan har irin wannan mugun laifi zai rika wakana ba tare da an gane ba a unguwar da ke kusa da babban birnin Enugu, wannan na nuna cewa lallai akwai bukatar a  binciki al’amuran tsaron jihar.
“Al’amarin nan akwai tada hankali, domin na ga gawarwakin nan. Lallai ne jami’an tsaro su yi kokari wajen tona asirin muggan da ke da hannu cikin wannan aika-aika domin gurfanar da su gaban shari’a, a hukunta su domin abin ya zama ishara. Wannan kisan kan akwai mugunta a cikinsa.” Inji Sambo.
Haka ita ma kungiyar kare hakkin dan Adam ta CRRAN da ke da mazauni a Enugu, ta nemi gwamnati ta dauki matakin bunkasa al’amuran tsaro a jihar. Haka kuma sun bukaci a gudanar da binciken kwakwaf game da wannan kisan gilla da ake wa mutane. Shugaban kungiyar, Barista Olu Omotayo, ya nemi  gwamnati da ta tsaftace unguwar Ugwuaji, a kawar da gawarwakin da ke wari domin kare lafiyar al’umma.
Shi kuwa Babban Limamin Babban Masallacin Enugu, Sa’eed, nasiha ya yi wa iyalan mamatan, inda ya ce su dauki hakuri, tare da jawo hankalinsu da ayar Allah da ke cewa “Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma.”