Kisan ’Yan Mauludi: Bala’in ya yi wa ’yan Arewa yawa —Bello Yabo

Sheikh Muhammad Bello Yabo ya bayyana alhilinsa kan yadda ake kashe al’ummar Arewacin Najeriya inda ya ce bala’in ya yi yawa

Kisan ’Yan Mauludi: Bala’in ya yi wa ’yan Arewa yawa —Bello Yabo

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Bello Yabo ya bayyana alhilinsa kan yadda ake kashe al’ummar Arewacin Najeriya inda ya ce bala’in ya yi yawa.

Ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da yake tsokaci kan kisan da jirgin soya ya yi wa masu taron Mauludi a garin Tudun Biri a Jihar Kaduna.

Malamin ya ce, “ga ’yan ta’adda sun addabi ’yan Arewa, ga yunwa sannan kuma ga sojoji na kisa da sunan kuskure.”

Don haka sai ya roki ’yan Arewa da su tashi tsaye su cire hassada da bakin ciki wajen kare martabarsu ta hanyar hada kansu, su rika magana da murya daya.

“Allah Ya isar wa bayin Allah da aka kashe, Allah Ya gafarta musu.

“Wannan kisa Allah Ya sa ya zama kaffarar zunubansu, Allah Ya sa iyakan wahalarsu ke nan.

“Amma tsakani da Allah bala’i ya yi mana yawa mu ’yan Arewa. Jama’a ’yan ta’adda su kashe mu, yunwa ta kashe mu, Sannan kuma sojojin da ya kamata su kare mu da dukiyarmu su zo suna kashe mu.

“Zafin ya yi mana yawa, bala’in ya yi yawa. Wa za ka fada wa in ba Allah ba?

“Kuma muna fada masa Allah ga fa halin da muka tssinci kanmu, Allah Ka kawo mana mafita,” in ji shi.

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira