Kisar miji: Ko ’yan uwan Bilyaminu sun yafe hukuma ba za ta kyale ba – ’Yan Sanda
A daidai lokacin da wadansu ke yada jita-jitar cewa iyayen marigayi Bilyaminu Bello da ake zargin matarsa Maryam Sanda da yi masa kisan gilla, wani dan uwan marigayin da ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu mahaifin marigayin, Alhaji Bello Halliru, bai yi magana daga inda yake jinya a kasar […]

A daidai lokacin da wadansu ke yada jita-jitar cewa iyayen marigayi Bilyaminu Bello da ake zargin matarsa Maryam Sanda da yi masa kisan gilla, wani dan uwan marigayin da ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu mahaifin marigayin, Alhaji Bello Halliru, bai yi magana daga inda yake jinya a kasar waje ba dangane da kisan dansa da aka yi ba.
Wannan ya kawo karshen yamadidin da wadansu mutane suke yi cewa iyayen marigayin sun yafe kisan marigayin.
Sannan wadansu ’yan sanda da layuyoyi da Aminiya ta tuntuba da su ma suka nemi a sakaye sunayensu sun ce ko da iyayen marigayin sun yafe, hukuma ba za ta yafe ba, domin za ta bi hakkin kashe dan kasarta da ake zargin matarsa da aikatawa.
Kuma wata majiya mai karfi ta ’yan sandan ta ce tuni ’yan sanda suka gano kyamarar daukar hotunan bidiyo ta CCTb da ke gidan ma’auratan. “Mun samu damar gano faifan bidiyon kuma ya nuna wadda ake zargin da wadansu masu gadi suna shigar da shi cikin wata mota inda daga nan suka kai shi asibiti,” inji majiyar.
Sannan wata majiyar ta ce ’yan sanda sun kama masu gadin, kuma Kakakin Rundunar ’Yan sandan Birnin Abuja, DSP Anjuguri Manzah wanda ya tabbatar da kama wacce ake zargin ya ce sun kama karin wadansu da ake zargi. Ya shaida wa majiyar cewa “Na san an kama karin wadanda ake zargi, amma ban san su wane ne ba, kuma ba zan iya tabbatar da cewa an samu faifan bidiyon CCTb ba, amma yana iya zama wani bangare na shaidar da ake tattarawa domin taimaka wa bincike.
Rundunar ’Yan sandan Birnin Tarayya dai har ta riga ta gurfanar da Maryam Sanda a gaban Babbar Kotu ta 32 da ke Jabi, Abuja, kan zargin yi wa mijinta Bilyaminu Bello kisan gilla.
Kakakin Rundunar Anjuguri Manzah ya ce, kotun ta tura wadda ake zargin zuwa gidan maza na mako biyu don ba ’yan sanda damar kammala gudanar da bincike.
Ya ce, hakan ya zama wajibi saboda wadda ake tuhumar tana da ’ya mai wata shida wanda hakan ya sa yana da wahala a tsare ta.
Ya ce tuhumar da aka gabatar ta dogara ce kan binciken farko, kuma idan aka kammala bincike ana iya gyara tuhumar ko kuma za a hada da wadansu da ake zargi. Ya ce, akwai wadansu da aka gayyata don yi musu tambayoyi a kan lamarin.
Kashe marigayi Bilyaminu Bello, dan tsohon shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Bello Halliru da ake zargin matarsa Maryam Sanda da aikatawa ta jefa jama’a da dama a cikin taraddadi da alhini.
Maryam Sanda dai ’yar Hajiya Maimuna Aliyu ce wadda ta taba shugabantar BankinAso Sabings, wadda aka so nada ta wakiliya a Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kasa (ICPC) kafin a dakatar da sunanta, bisa zargin ta da yin alumdahana da Naira miliyan 57 na wasu filaye da ta sayar, kisan da ake zargin ’yarta Maryam da yi ga mijinta Bilyaminu yana ci gaba da jawo muhawara da cece-ku-ce musamman a kafofin sada zumunta na zamani.
Mahaifin marigayin Alhaji Bello Halliru ya kuma taba zama Mukaddashin Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP ta kasa daga shekarar 2015 zuwa 2016; kuma ya yi Ministan Tsaro daga 2011 zuwa 2012 kuma kafin nan ya yi Ministan Sadarwa daga shekarar 2001 zuwa 2003.
Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa marigayi Bilyaminu Bello da Marryam Sanda, sun fara soyayya ne fiye da shekara goma da suka wuce lokacin da take karatu a Jami’ar Maiduguri, kamar yadda wata majiya ta shaida wa Aminiya.
Kuma duk da Bilyaminu ya auri wata mace amma sai ya sake ta cikin shekara daya, inda ake zargin cewa Maryam ce ta ce ba za ta zauna da kishiya ba, don haka ya saki matarsa kafin ya aure ta, kuma ana zargin ita ta karbi takardar sakin ta kai wa matarsa tasa a lokacin.
Bayanai sun ce bayan an yi auren an yi bikin na garari inda aka kwashe kwanaki ana dabdala a birnin Abuja, kafin ango da amaryar su tare a Rukunin Gidajen ’Yan Fensho na Kamfanin NNPC da ake kira ‘NNPC Pension Estate’ da ke titin Pakali a Unguwar Wuse 2, Abuja, inda kuma a nan ake zargin matar tasa ta kashe shi.
Sau hudu Maryam tana yunkurin kashe mijinta Bilyaminu – Shaidu
daya daga cikin abokan marigayin mai suna Habib Gajam (da ake kira da Gidado), ya fadi dalla-dallar yadda lamarin ya faru a shafinsa na tweeter da aka buga a sashin Lifestyle na kafar labarai ta inside are wa.com.ng, inda ya ce: “A yau na ga mafi munin rashin tausayi da nuna tsabagen rashin kunya da girman kai game da batun rasuwar Bilyaminu.”
Ya kara da cewa: “Da misalin karfe 9-10 na daren da ya gabata (Asabar), an samu tashin hankali a tsakanin Bilyaminu da matarsa Maryam a gidansa. Maryam ta bukaci ya sake tare da yi masa barazanar za ta yanke masa mazakuta idan ya ki. Ibrahim Aleiro, abokin Bilyaminu (wanda a gabansa aka fara takaddamar) ya shiga tsakaninsu har sau hudu domin hana Maryam ta daba wa mijinta kwalba. Ibrahim ya kira Auta (Kawun Maryam) da kuma Abba (dan uwan Bilyaminu) wanda ya bar gidan kafin takaddamar ta barke cewa su zo su shiga tsakani. Bayan kura ta dan lafa sai Maryam ta fasa wata kwalbar gyada ta sake yin yunkurin daba wa Bilyaminu, amma a wannan lokaci sai ya rike hannuwanta ya yi kokarin kwace kwalbar daga gare ta, inda ya samu rauni a kokarin yin haka, sai ta cije shi a yatsa.”
Ya ci gaba da cewa, “Kawu Auta ya iso a wannan lokaci ya kwantar da kurar, inda su biyun suka yi wa Kawu Auta alkawarin komai ya wuce. Kuma bayan kura ta lafa ne Bilyaminu da abokinsa suka tafi kemis aka yi masa maganin cizon da Maryam ta yi masa a hannu. Daga nan suka wuce na’urar ATM ya ciro kudin domin biyan sauran kudin gyarar motar Maryam da ta samu hadari. Zuwa karfe 11 na dare Bilyaminu da Ibrahim sai suka koma gidan. Abba (dan uwan Bilyaminu) ya iske su a dakin karbar baki. Sun zauna har tsakiyar dare kafin ya yanke shawarar komawa gida ya kwanta.”
Gajam ya bayyana kalmomin ban-kwana da Bilyaminu ya yi ga dan uwansa da sauransu kuma ya bayyana kokarin da Maryam ta yin a sauya labarin a ofishin ’yan sanda domin ta boye laifinta.
Shaidar ya ce: “Lokacin da Bilyaminu yake musu ban kwana ya shaida wa Ibrahim cewa, “Ba zan koma ba, har sai ta yi barci. Suka yi ban kwana Abba da Ibrahim suka tafi. “Wajen karfe 2 na ranar Lahadi, sai aka gayyaci iyalansu zuwa Asibitin Maitama, inda Bilyaminu ke kwance a cikin jini da kuma sarar wuka a wurare da dama a kirjinsa da kafadarsa da wani mugun rauni a cinyarsa da wurare da dama da aka cije shi a cikinsa.”
Ya ce, “Maryam ta yi ikirarin daba masa wuka ga mahukuntan asibitin. Kuma batun zai gusa zuwa ofishin ’yan sanda na Matama. A ofishin ’yan sanda na Maitama da aka nemi Maryam ta rubuta bayaninta sai labari ya canja. Ta ce sun yi fada ne da Bilyaminu ya samu rauni daga fasasshiyar kwalbar Shisha kuma ba ta daba masa wuka ba.”
Ya kara da cewa: “Daga nan aka dauke ta zuwa Hedkwatar Rundunar ’Yan sanda ta Abuja da ke Garki II don ci gaba da bincike. Kwamishinan ‘’Yan sanda ya bayar da umarnin a ziyarci inda aka yi barnar. Kuma abin da ya ba Abba (dan uwan Bilyaminu) da Ibrahim (abokinsa) wadanda su shaidu ne a binciken, shi ne an iske an wanke jinin da ke dakin, kuma makamin da aka yi amfani da shi ya bace, amma tukunyar fulawa da ta Shisha suna fashe don hakan ya dace da bayanin da Maryam ta yi a ofishin ’yan sanda.
A daidai lokacin da ake tsakiyar wannan abin bakin ciki da tashin hankali, Maryam ta iya samun karfin halin da za ta canja bayaninta. Abin da ya fi daga hankali, shi ne yadda ba ta nadama kuma ba ta girmama iyalan marigayin. Mutumin da ya saki matarsa ta farko don ya zauna da ke bai cancanci wannan ba. Allah Madaukaki zai yi wa Bilyaminu sakayya a Ranar kiyama. Allah Ya saka wa Bilyaminu da Aljanna kuma Ya albarkaci rayuwar ’yarsa mai wata takwas wato Sa’adatu.”
Makwabtan ma’auratan sun ce ma’auratan suna yawan yin fada a tsakaninsu, kuma ranar Asabar din sun yi mummunan fada bayan da Maryam ta dauki wayarsa inda ta ga sakon da wata ta aiko masa tana cewa: “Na godew da tadi/ganawar da muka yi jiya.”
Makwabtan da ba su son a fadi sunansu, sun ce suna zargin Maryam ta daba masa wuka inda ya suka ji yana cewa “Maryam ki taimake ni,” ita kuma tana cewa “Alhaki ya kama ka.” Daga nan sai ta fito ta nemi makwabta su taimake ta a sa shi a mota don a kai shi asibiti. An ce asibitoci biyu da suka fara zuwa sun ki karbarsa ganin munin halin da yake ciki, kuma a Asibitin Maitama ne aka kira ’yan sandan da ke aikin tsaronasibitin don su kira magabatansu kan lamarin, saboda ganin an daba masa wuka a kirji da kafada da cinyarsa ga kuma cizo a cikinsa yana cikin jini. Majiyar ta ce Maryam ta furta wa ’yan sandan cewa ita ta daba masa wuka, amma da aka kai ta ofishin ’yan sandan Maitama, aka ce ta rubuta bayanin abin da ya faru, sai ta sauya abin da ta fada a asibiti, ta ce sun yi fada ne ya fadi a kan kwalbar tabar Shisha ya ji ciwo, amma ita ba ta daba masa wuka ba.
Bilyaminu Bello mai shekara 35, an yi masa Sallar jana’iza a ranar Litinin da ta gabata a Babban Masallacin kasa da ke Abuja kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Wata majiya mai karfi ta ce mahaifiyar Maryam, Hajiya Maimuna Aliyu ta dauki wani babban lauya don ya kare ’yarta Maryam Sanda kan wannan zargi.