Kishi ya sa muka kafa kungiyar Kano LEADS – A’isha Dankani

kungiyar Kano Leadership Empowerment and Adbocacy for Debelopment, wato Kano LEADS mai taken ‘DA RUWANA A DUK ABIN DA YA SHAFI JIHAR  KANO’ kungiya ce da wadansu ’yan asalin Jihar Kano suka kafa da niyyar lalubo hanyoyin ciyar da jihar gaba tare da dakile abubuwan da suke barazana ga ci gabanta. Barista A’isha Ibrahim dankani […]

Kishi ya sa muka kafa kungiyar Kano LEADS – A’isha Dankani

kungiyar Kano Leadership Empowerment and Adbocacy for Debelopment, wato Kano LEADS mai taken ‘DA RUWANA A DUK ABIN DA YA SHAFI JIHAR  KANO’ kungiya ce da wadansu ’yan asalin Jihar Kano suka kafa da niyyar lalubo hanyoyin ciyar da jihar gaba tare da dakile abubuwan da suke barazana ga ci gabanta.

Barista A’isha Ibrahim dankani wacce tsohuwar ma’aikaciya ce a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano da kuma Gwamnatin Tarayya ce Shugabar kungiyar ta Kano Leads, ta shaida wa Aminiya cewa kishi da damuwa da Jihar Kano ne ya sa suka himmatu wajen ganin kungiyar ta kafu tare da yin aiki tukuru  wajen ganin ’yan jihar sun amfana daga ayyukan gwamanti a kowane fanni na rayuwar al’umma.

“Jihar Kano ta samu kanta a cikin halin ha’ula’i, an ce a Jihar Kano ce aka fi mu’amala da miyagun kwayoyi, ga rashin aikin yi da ya yi wa matasa katutu, ga rashin ingantattun makarantu ga matsalolin siyasa. Ban taba ganin garin da ake yin fyade kamar Kano ba, domin Kwamishinan ’Yan sanda ya ce a cikin wata daya kawai an samu rahotannin aukuwar fyade sama da 300. Wannan ba karamin abin damuwa ba ne. Kasuwanci da aka san Kanawa da shi ya tabarbare, yanzu  idan ka ga kasuwanci mai kyau a Kano, to ba na ’yan jihar ba ne. 

“Ada muna yara harkoki ake yi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano. Yanzu fa? Wata rana jirgi daya tak zai zo. A yanzu  idan mutum 100 zuwa 200 za su je Dubai sai sun tafi ta Legas wanda hakan ba karamin ci baya ba ne gare mu, domin sai mutum ya kara biyan kusan Naira dubu 80 ga kuma kudin kwanan otel da na abinci wanda Jihar Legas ke amfana da wannan tagomashi. Idan ka duba duk titunanmu almajirai za ka gani. 

“A fannin siyasa sai wanda aka dauko aka dora mana. Ba zai yiwu mu ci gaba da rungume hannu mu zura ido muna kallo abubuwa suna kara tabarbarewa ba.”

Shugabar ta ce sha’anin ci gaba a kowace al’umma ba abu ne da ya dogara a hannun shugabanni ba, abu ne da dole sai al’ummar da kanta ta tashi tsaye ta taimaka wa kanta  “Allah Ya albarkaci Jihar Kano da mutane masu ilimi wadanda za su iya kawo duk wani abu na ci gaba tare da dakile abubuwan da ke kawo ci baya a harka rayuwa.  kofa a bude take ga duk wanda yake ji da ruwansa a duk abin da ya shafi Jihar Kano ya zo a yi wannan tafiya tare da shi. Mu sa hannu mu daga Jihar Kano tare da dago duk wanda yake so taimakon jihar.”

Da take lissafa ayyukan da kungiyar ta fara, ta ce  kungiyar ta yi ruwa-da-tsaki game da shirin samar da aikin yi na NPOWER “Da muka ga sunan da aka fitar, muka ga mu da muke da yawa mu ne kuma wadanda ’yan jiharmu ba su samu aikin da yawa ba, ga wasu jihohin da yawansu bai fi wata karamar hukuma a Kano ba, amma sun samu kaso mafi tsoka na aikin, sai muka kai kuka ofishin Shugaban kasa inda kuma aka share mana hawaye, da aka sake yin kashi na biyu jama’ar Jihar Kano sun samu. Haka kuma Kano LEADS tana yin ruwa-da-tsaki wajen ganin gwamnati ta yi wa jama’ar jihar aikin da suke bukata, misali da muka samu labarin za a yi titin jirgin kasa mun nuna wa gwamnati cewa akwai abubuwan da ’yan Kano ke bukata fiye da wannan, musamman magance shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa tare da samar musu da aikin yi. Alhamdulillahi gwamnati kuma ta saurare mu.”