Kishi ya sa shi daddatsa wanda suke takara a kan budurwa
Sai dai tuni matar da ake takaddamar a kanta ta cika wandonta da iska.
’Yan sanda a Jihar Ogun sun cafke wani matashi mai suna Bisi Omoniyi kan zargin hallaka wani mutum mai shekara 50 a kan budurwa.
Rahotanni sun ce matashin, mai kimanin shekara 25 ya kashe mutumin, Akinyemi Wahab Alani, ne ta hanyar daddatsa shi da adda a gidan budurwar tasa.
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 11 a Kwara
- Najeria A Yau: Rikicin Majalisar Malaman Kano ya bar baya da kura
Dubun matashin ta cika ne bayan ’yan sandan yankin Owode Egbado sun sami korafi kan aikata danyen aikin a garin Ajilete da ke Karamar Hukumar Yewa ta Arewa a Jihar.
Kakakin ’yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da hakan yayin zantawarsa da manema labarai ranar Lahadi.
Ya ce da jin hakan ne baturen ’yan sandan yankin, DPO Owode Egbado bai yi wata-wata ba ya aike da jami’ansu inda suka kama wanda ake zargin.
Ya ce likitoci sun tabbatar da mutuwar mutumin lokacin da aka garzaya da shi asibiti.
A cewar Oyeyemi, binciken farko-farko ya nuna cewa Akinyemi ya ziyarci matar ne mai suna Kafayat Sakariyau a garin na Ajilete da nufin ya kwana a wajenta.
Ya ce wanda ake zargin, wanda shima yake alaka da matar ya ziyarceta kwana daya kafin faruwar lamarin amma aka hana shi shiga.
Oyeyemi ya ce sai dai Bisi ya sake dawowa inda ya kutsa kai cikin dakin, inda ya tarar da mamacin a yanayin da ya ce ba abin lamunta ba ne a wajensa.
Hakan ne ya jawo kace-nace wanda ya kai ga fada a tsakaninsu, har shi Bisin ya yi nasarar daukar wata adda a dakin ya daddatsa Akinyemin har sai da ya mutu.
Ya ce tuni aka aike da gawar mamacin zuwa asibiti domin fadada bincike kan musabbabin mutuwar.
Sai dai ya ce tuni matar da ake takaddama a kanta ta cika wandonta da iska.