Kishi ya sa wata mata ta kona kishiyarta da ’yarta a Taraba
Tsananin kishi wata mata, mai suna Talatu Gazabu yasa ta kona kishiyarta mai suna Habiba Adamu da tafasshshen ruwan zafi a kauyen Gazabu, karamar hukumar Bali, Jihar Taraba. Ta faki idon matar yayin da take zaune da sauran kawayenta da suka zo sada zumunci wurinta, kamar yadda Aishatu Ayuba Mshelia ta tabbatar wa Aminiya bayanin […]
Tsananin kishi wata mata, mai suna Talatu Gazabu yasa ta kona kishiyarta mai suna Habiba Adamu da tafasshshen ruwan zafi a kauyen Gazabu, karamar hukumar Bali, Jihar Taraba. Ta faki idon matar yayin da take zaune da sauran kawayenta da suka zo sada zumunci wurinta, kamar yadda Aishatu Ayuba Mshelia ta tabbatar wa Aminiya bayanin aukuwar lamarin a Kalaba.
Bayanin musabbabin kona kishiyar da muka samu shi ne kishin haihuwa kada amaryarta Habiba ta haihu da mijin su mai suna Adamu, domin ita uwargidan, wato wadda ta kona kishiyar ta, an ce tana da ’ya’ya biyar yayinda ba ta son amaryar ta haihu da mijinsu, an ce lokuta da dama idan amarya Habiba , wadda aka kona ta samu ciki ba ya kaiwa wani tsawon lokaci sai ya zube, lamarin da ya rika jawo ayar tambaya da wasu mutane, har ma ake ganin ko uwargidan ce ke da hannu wajen yin surkulle cikin ke barewa idan an samu
“Domin ita uwargidan wadda ta kona amaryarta tana da ’ya’ya biyar ita kuma wannan da aka kona ’ya daya gareta, shi ne uwargidan ta kwara musu ruwan zafi” inji Aishatu.
Tun Farko an rika zargi rashin son zama da kishiya ce da mijin su ya yi mata ya kaita ga daukar wancan mummunan mataki na kona kishiyar ta, domin ita ta samu gindin zama da mijin su, al’amarin da ga shi ya sanya ta jefa kanta cikin matsala tsakanin ta da mijinta da iyayen amaryar da hukuma.
“ Ita amaryar Habiba ta dawo daga gidansu da taje gaida iyayenta ta can kauyen su ta dawo. Mako daya da dawowarta gidan mijin ne mutane na zuwa yi mata barka da kuma sannu da dawowa, sai uwargidan mai suna Talatu ta je ta tafasa ruwan zafi a wata unguwar ta zo da shi kamar wata wadda ta je unguwa ta sayo wani abu, ta shigo da shi gida, shigowarta gidan ke da wuya ta iske amaryar ta zaune tare da wasu baki ba tare da bani lokaci ba, sai ta watsa mata ruwan zafin a jiki ragowar kuma ta watsa jikin yarinyar da take shayarwa, inda suka kone. Abin dai babu kyawun gani, duka jikin su fatar ta sabule”injita.
Mutum uku duk da bakuwar wadda aka kona ce suka hadu da hadarin “daga fuskarta zuwa nonon ta duka sun kone da ruwan zafi ’yarta kuma kama daga jikinta fuskarta har zuwa gadon bayanta duka ya kone.” Injita.
Aishatu Ayuba Mshelia, ta ce, ganin cewa uwargidan kishiyarta ta yi niyyar konawa da wannan manufa, ta shigo gidan tsautsayi da kaddara ta sanya tafasasshen ruwan zafin ya samu wata daga cikin matan da suka zo ziyara, sai ta ba ta hakuri, ta ce ayya baiwar Allah yi hakuri ba ke na yi niyya ba ruwan ya sameki, uwargida Talatu ta roki afuwarta. Da ta watsa wa kishiyarta Habiba ruwan zafi a jiki, an ce zakara ya bat a sa’a , kuma yanzu haka amaryar da aka kona tana asibitin Bali ana ba ta kulawa ta musamman domin ceto rayukan su ita da ’yar ta.
Mshelia , ta kara da cewa bayan da mai lafin da ake zargi ta cikata aikinta ta kuma gudu, yanzu haka iyayen mai laifin da ake zargi suna hannun hukumar ’yan sanda. Wakilinmu ya yi kokarin samun wani daga cikin jami’an ’yan sandan garin Bali domin jin inda aka kwana da wannan batu, amma duk kokarin ya ci tura. Sai dai wata majiya a kauyen Gazabu, ta tabbatar da cewa ko da ma za a iya yin wani abu har sai anga uwa da ’yarta sun samu lafiya, sun dawo hayyacin su, tunda wadda ta aikata laifin ta gudu.