Kishi ya sanya ni sayar da Aminiya a Fatakwal – dan Rabi
Wani mai sayar da kaset da jaridar Aminiya a babbar mayankar Fatakwal da ke titin Trans Amadi mai suna Muhammed dan Rabi ya ce kishi ne ya sanya shi sayar da jaridar Aminiya baya ga kasuwancinsa da aka san shi da shi tsawon zamansa a mayankar. A hirarsu da wakilinmu dan Rabi ya ce an […]

Wani mai sayar da kaset da jaridar Aminiya a babbar mayankar Fatakwal da ke titin Trans Amadi mai suna Muhammed dan Rabi ya ce kishi ne ya sanya shi sayar da jaridar Aminiya baya ga kasuwancinsa da aka san shi da shi tsawon zamansa a mayankar.
A hirarsu da wakilinmu dan Rabi ya ce an haura shekara biyu ana kai Aminiya mayankar kuma wa shi ne ake kawo ta. dan Rabi ya ce a da can ana kawo kamar kwafe 20 zuwa 25 amma yanzu haka kwafe 40 ake kai masa.
Ya ce matsalar da makaranta jaridar ke korafi a kai ita ce wani lokaci suna ganin labaran da ya kamata a sanya hoto to amma sai su ga ba a sanya, ko kuma su ga sunan mutum ba hotonsa koda karami.
Ta fuskar cinikin jaridar ya ce mutane sun raja’a sosai suna sayenta, “Hakika Aminiya ta yi fice sosai a cikin Fatakwal,” inji shi, inda ya ce hatta mutanen yankin da ba sa jin Hausa sukan yi sha’awar jaridar musamman idan suka ga hoton dan yankinsu, sai su ce suna so amma ba su iya Hausa ba.
Ya ce daya daga cikin shafukan da suka fi burge shi da wasu makaranta jaridar a Fatakwal shi ne shafin Dodorido, to amma suna takaicin da wani lokaci sai a yi wata daya ba a sanya shi ba. “Jama’a na kawo mana korafi, wasu suna cewa matukar suka karanta jaridar ba su karanta Dododrido ba, ba su farin ciki da haka. Sannan sai shafin Mu sha Dariya da na wasanni yake son da sauransu,” inji shi.
Ya ce su ’yan Arewa mazauna Kudu ba su cika samun labarin abin da ke faruwa a Arewa Ba sai sun sayi jaridar Aminiya suke samun labari cikakke saboda koda rediyo ne aka kama BBC ko Muryar Amurka ba su samun cikakken labarin Arewa, gara Rediyon Faransa.
dan Rabi wanda ya ce shi mutumin Makera da ke kusa da Birnin Kebbi a Jihar Kebbi ne, ya ce saboda Aminiya ya kan hau babur daga kauyensu ya je har Birnin Kebbi ya saya ya koma gida. “Kuma akwai wanda kowace Lahadi sai ya zo gida wurina ya ji ko na sayo jaridar don ya karanta, jaridar ba ta isar mu a Jihar Kebbi ko a Birnin Kebbi ana korafin ba ta isarsu bare su yi tunanin kai wa wani yanki ko karamar hukuma,” inji shi.