Kishin Kasa: Idan babu kasa babu rayuwa
Tare da sallamar da muka saba, ya ku masu bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma muna dauke da sabon maudu’i ne, wanda zai yi mana tambihi game da kishin kasa da kuma muhimmancinsa ga al’umma. A matsayinmu na ’yan kasa, ya dace mu gane muhimmanci da tasirin kishin kasa […]
Tare da sallamar da muka saba, ya ku masu bibiyar wannan shafi na Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma muna dauke da sabon maudu’i ne, wanda zai yi mana tambihi game da kishin kasa da kuma muhimmancinsa ga al’umma.
A matsayinmu na ’yan kasa, ya dace mu gane muhimmanci da tasirin kishin kasa da kuma dangantakar da ke tsakanin kasar tamu da kuma mu kanmu al’ummar cikinta.
Abu na farko da ya kamata kowane dan kasa ya gane shi ne, kasarka ita ce alkiblar rayuwarka. Abin nufi a nan shi ne, duk dai inda kake zaune, a cikin kasar nan kake. Ya Allah kana cikin kauye ne ko a birni, kai dan kasa ne, domin kuwa kana zaune ne a unguwarku, wacce ke a karkashin k aramar hukuma, a karkashin jiharku; wadanda su kuma suke a cikin Najeriya.
Kasancewar ba ka da wata kasa da ta kai kasarku, lallai ne ka maida hankali wajen nuna kishinta da kare martabarta, domin kuwa idan ta kasance mai muhibba da martaba, to kai ne ka zama mai martaba da muhibba. Idan kuma ta zama ballagaza, marar kima a idanun duniya, to ka sani kai ma haka kake.
Domin ganin ka zama mutum nagari, mai kima da martaba, sai ka tashi tsaye, ka yi kokari iya yin ka, wajen bunkasa kasarka. Dalili na farko ke nan da ya sanya za ka zama mai kishin kasa. Amma idan zan kara yin wata tambayar kuma, ta yaya za ka zama mai kishin kasa? Ta yaya kishin kasarka zai amfane ka, ya amfani al’ummar kasarka da kuma ita kanta kasar?
Yana daga cikin kishin kasa, ka kasance mai gaskiya da amana a cikin al’amuranka. Idan ka kasance mai fadar gaskiya kuma kana aiwatar da al’amuranka cikin gaskiya; sannan kuma ka kasance mai rikon amana wajen mu’amalarka da mutane, to kuwa kasarka za ta zama mai gaskiya da amana, abar kauna ga al’ummar duniya. Dalili shi ne, a matsayinka na dan kasa, ka zama jakadanta mai gaskiya da amana. Idan kai ka zama haka, wancan shi ma ya zama haka, ita ma waccan ta zama haka; shi ke nan an samu abin da ake so. Kasarmu za ta cika da masu gaskiya da amana ke nan, wanda haka zai sanya ta zama amintatta kuma mai aminci a cikin kawayenta na sassan duniya.
Kishin kasa ne ga dan kasa ya kasance mai neman na kansa, wato kada ya kasance mai zaman banza, wanda ba ya aiki ko sana’ar komai. Da zarar dan kasa ya zauna durshan ba tare da yana wata harka ba, babu wanda zai zame masa aboki sai Shaidan. Wannan zaman banza zai bijiro masa da tunane-tunane marasa kyau, sannan su ingiza shi zuwa aikata munanan ayyuka, wadanda za su kasance halaka a gare shi kuma wadanda za su cutar da sauran al’umma. Daga nan kuma sai al’amarin ya shafi kasarsa, domin kuwa sunanta zai baci ta hanyar munanan ayyukansa.
Don haka, ya dace mutum ya mike tsaye ya sama wa kansa abin yi. Kada mutum ya ce zai zauna sai ya samu wani babban aiki ko babbar sana’a. Koda ka gama jami’a ne, idan ba ka samu aiki ba, yi kokari ka fara koda aikin karfi ne na kwadago. Dan abin da za ka samu, zai iya zama mai albarka kuma ka biya bukatarka da shi. Kada ka yi mamaki, ta hanyar wannan yunkuri da ka yi na aikin karfi, Allah na iya hada ka da wata sila, wacce za ka iya samun aikin da ya fi shi.
Haka kuma, za ka iya fara kasuwanci koda da karamin jari ne. Misali, za ka iya fara sayar da katin waya. Sannu a hankali, daga ’yar ribar da za ka rika samu, madamar kana adanawa da kadan-kadan; jarinka yana iya zama mai girma. Idan dai har ka rika gudanar da harkarka cikin gaskiya da tsare hakkin jama’a, kasuwancin naka yana iya zama mai albarka. Domin kuwa, akwai mutane da yawa da suka fara kasuwanci da kankanen jari kuma suka bunkasa har suka zama hamshakan ’yan kasuwa.
Ala-ayyi-halin dai, zaman kashe wando, ko zaman jiran mai yawan da ko alamarsa babu, alhali babu tabbas, ba abin dogaro ba ne. Don haka, kishin kasa ne ga mutum ya hana kansa zaman kashe wando, ya cire girman kai daga zuciyarsa, ya yunkura domin neman na halal komai kankantarsa.